'Gurbacewar muhalli tamkar shafe al'umma ne'

Dakta Santamu ya tsere Uganda a 1974 kuma ya zama babban limamin coci a 2005

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dakta Sentamu ya tsere Uganda a 1974 kuma ya zama babban limamin coci a 2005

Babban limamin cocin York, na biyu mafi matsayi a Ingila, ya bayyana gurbacewar muhalli a jihar Bayelsa da ke yankin Neja Delta mai arzikin man fetur a Najeriya a matsayin wani kisan kiyashi da ya shafi muhalli.

A wata hira ta musamman da BBC, Dr John Sentamu ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya da al'ummar duniya su kara kaimi wajen rage barnar da malalar man fetur ke haddasawa a yankin.

"Mutane na magana kan gurbacewar muhalli. A ganina, na duba muhalli kuma na duba rayuwar mutane kuma na fahimci cewa wannan tamkar wani kisan kiyashi ne ga muhalli," a cewar Dakta John.

Babban Limamin, wanda ke jagorantar wani kwamiti da ke bincike kan illar ayyukan kamfanonin mai a jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya, ya ce ba za su amince da halin-ko-in-kula daga kamfanonin ba.

Ya kuma ce dole ne su dauki alhakin malalar da mai ke yi daga kayan aikinsu.

Dakta Sentamu ya zargi gwamnatin Najeriya da kin daukar alhakin kare muhallin Bayelsa.

"Na fito daga Uganda kuma yanzu ina zaune a Birtaniya, amma ai duniyar ta zama daya yanzu. Al'umar Bayelsa tamkar makotana ne. Na damu matuka da lafiyarsu.

"Sannan idan kuka ga talaucin da suke ciki, a kasar da ke ke da arzikin man fetur abin na da ban mamaki."