Yadda rikicin Kamaru ke shafar matafiya

Kamaru

Asalin hoton, COLBERT NKWAIN

Rikicin yankin Ingilishi na Kamaru ya janyo kudin abubuwan hawa ya rubanya sau hudu inda hakan yake hana mutane yin tafiye-tafiye.

An fara rikicin ne a shekarar 2016, kuma ya shafi yadda mutane ke tafiye-tafiye da karuwar hadurra a yankin arewa maso yammacin kasar.

Wani wanda ya je Bamenda daga garin Tatum ya shaida wa BBC yadda ya wahala a yayin tafiyar tasa.

"Na hau babur daga Tatum na iso Kumbo kuma na biya FCFA 5000 sannan na hau mota daga Kumbo na zo Bamenda na biya FCFA 10,000."

"A baya da FCFA 1000 zan iya hawa mota in je Kumbo daga Tatum."

"Wannan lamarin ya munana saboda dan kudin da muke da shi duk ya kare a kudin mota. Idan a baya muna ganin kudin motar ya yi yawa yanzu muna biyan sau hudunsa, to ai ko abin ya lalace."

Wata mata da ba ta so a bayyana sunanta ta ce abin da ya sa kudin abun hawa ya yi yawa shi ne saboda direbobi na biyan cin hanci ga mayakan a ware a hanya.

Ta ce "A lokacin da muka kamo hanya daga Jakiri za mu je Bamenda, na biya FCFA 11,000 saboda ina da kaya. Da muka isa Bamenda sai direban ya ce min kudin nan da na biya shi sun kare a biyan cin hanci".

'Yan a ware wanda ake kira "amba boys" na da tsaya wa a kan tituna rike da bindigogi kuma suna rufe fuskokinsu.

Idan direba bai ba su cin hanci ba, su kan lalata masa motar, wani lokaci direban kan biya daga baya idan ba su da kudin.

Idan suka ji labarin cewa jami'an tsaro na tafe, sai su shiga daji su boye amma wani lokaci a kan mamaye su a kashe su, in ji matar.

Asalin hoton, REINNER KAZE

Abin da ba ku sani ba kan rikicin 'yan awaren Kamaru

Daga Farouk Chothia, BBC News

Kungiyoyin Red Dragon da Ambazonia Defence Forces (ADF) - na cikin kungiyoyin da suka dauki makamai domin yakin neman 'yancin yankin masu amfani da turancin Ingilishi daga Kamaru.

Sun kasance wata babbar barazana ga zaben shugaban kasa da za a yi ranar Lahadi, zaben da Shugaba Paul Biya mai shekara 85 da haihuwa ke neman tsawaita wa'adin mulkinsa na shekara 36.

Kungiyoyin masu daukar makamai da suka bulla shekara daya da ta gabata, sun karbe ikon garuruwa da kauyukan yankin masu amfani da harshen Ingilishi na arewa maso yamma da kudu maso yamma daga hannun gwamnatin Kamaru.

Wannan abu ne da shekaru biyun da suka gabata ana iy cewa ba mai yiwuwa ba ne, inji Nna-Emeka Okereke, wani mai nazarin siyasar Kamaru:

"Suna da kimanin mayaka 500 zuwa 1,000, amma abu mafi muhimmanci shi ne suna da karfin gwuiwar gudanar da yakin neman 'yancin wani yanki da suke kira Ambazoniya.

'Muna alfahari da amfani da turancin Ingilishi'

Kungiyoyin mayakan sun fara samuwa ne a 2017 bayan da sojojin Kamaru suka dakile wata zanga-zangar mutanen yankin, wanda lauyoyi da malaman makaranta suka jagoranta.

Sun tuhumi gwamnatin kasar da danne 'yan asalin yankin, kana tana fifita masu amfani da harshen Faransanci wajen samar da ayyuka da guraben ilimi.

Kashi 20 cikin 100 na al'ummar Kamaru sun fito ne daga yankin masu amfani da harshen turancin Inglishi.

Bayan da wasu kungiyoyi suka ayyana 'yancin kai a ranar 1 ga watan Oktobar 2017, gwamnatin Kamaru ta yi watsi da kudurin nasu, kuma ta kira su 'yan ta'adda, kuma tashar rediyon Kamaru ta ce Shugaba Biya ya ce zai yake su.

Yakin ya yi sanadin rasa rayukan a kalla fararen hula 420, da 'yan sanda da sojoji 175 da daruruwan mayaka.

Fiye da mutum 30,000 kuma sun kauracewa muhallansu, inji kungiyar ta ICG.

Da alama Mista Biya ne zailashe zaben, domin shi ke da cikakken iko da sojoji da 'yan sandan kasar.

Amma tambaya a nan ita ce ko zai nemi sasantawa da kungiyoyin awaren bayan zaben.