Guguwar juyin-juya halin Larabawa ta dawo ne?

  • Daga Jeremy Bowen
  • BBC Middle East editor
Wani mai zanga-zanga a Iraqi yana daga tuta a Bagadaza ranar 29 ga watan Oktoba, 2019

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga na fitowa a kasashen gabas ta tsakiya, har da Iraqi

Yayin da yanayin zafi ke karewa a yankin Gabas ta Tsakiya, shin ko akwai yiwuwar a sake fadawa cikin wani zamani na juyin juya-hali?

A Iraqi, jami'an tsaro na harbe masu zanga-zanga da suka fito kan tituna, a Lebanon kuwa masu zanga-zanga sun tsayar da al'amurar kasar cik, inda suke kokarin wargaza gwamnatin firaminista Saad al-Hariri.

A Masar kuwa cikin makonnin da suka gabata ne jami'an tsaro suka murkushe yunkurin masu zanga-zangar adawa da 'yan sanda na gwamnatin Shugaba Abdul Fattah al-Sisi.

Akwai bambanci sosai tsakanin wadannan kasashe uku (Iraq da Lebanon da kuma Masar).

To amma masu zanga-zangar, musamman matasa, na da damuwa iri daya, a daukacin fadin kasashen Larabawa.

Kiyasi ya nuna cewa kashi 60 cikin 100 na yawan al'ummar yankin matasa ne kasa da shekara 30.

Yawan matasa zai iya zama abin alheri ga kasa, amma hakan zai samu ne idan an biya masu bukatunsu a bangaren tattalin arziki, da ilimi, da samar da abubuwan bukatun rayuwa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Matasa a Lebanon da Iraqi da ma wasu kasashen yankin sun fada tsundum cikin takaici, wanda ke rikidewa zuwa fushi.

Yawaitan ayyukan rashawa

Manyan abubuwan da ake kokawa a kan su, su ne rashawa da rashin aikin yi. Wadanda suke da alaka ta kut da kut.

Wata kididdiga ta nuna cewa Iraqi na daga cikin kasashe na gaba-gaba a duniya wadanda ke fama da matsalar rashawa.

Lebanon ma haka, sai dai bai yi kamari ba kamar na Iraqi.

Rashawa muguwar cuta ce da ke lalata makomar wadanda suka kamu da ita.

Mutanen da ke a yankunan da ake fama da rashawa kan fusata cikin kankanin lokaci, musamman a yanayin da hatta masu ilimi ba su iya samun aiki, mutane kalilan ne ke juya dukiyar kasa.

Idan ya kasance bangarorin gwamnati da kotuna da kuma 'yan sanda suka fada cikin matsalar rashawa - alama ce ta cewa al'amuran kasa sun tabarbare.

A Lebanon da Iraqi, baya ga neman shugabanni su sauka, al'umma na neman a sauya tsarin gwamnatin baki daya.

Inda matsalar take

Wani abu da ya fito fili game da Iraq shi ne rikici ya zama jiki a cikin al'umma.

A duk lokacin da masu zanga-zanga suka fito suna bore kan rashin aikin yi za ka ga jami'an tsaro sun bude wa mutane wuta da bindiga.

Yawancin zanga-zangar da ake gudanarwa a Iraqi, ana shirya su ne ba tare da jagora ba.

Sai dai fargabar da gwamnati kan yi shi ne idan abu ya yi kamari masu zanga-zangar za su iya samun jagorori wadanda za su sa zanga-zangar ta munana.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Zanga-zanga ta bazu zuwa birnin Karbala na Iraqi

Masu zanga-zanga kan mamaye yankuna ne da kan alamta ikon gwamnati, kamar yankin da ake kira 'Green zone' na birnin Bagadaza.

Yanki ne da a baya ya kasance a hannun Amurkawa. Yanzu kuma wuri ne da ke kunshe da ofisoshin gwamnati, da na jakadancin kasashe da kuma gidajen mashahuran mutane.

Zanga-zangar ta samo asali ne daga Bagadaza, inda ta watsu zuwa wasu yankuna.

A birnin Karbala, rahotanni sun ce an samu rashe-rashen rayuka da raunata mutane da dama lokacin da aka bude masu wuta.

Wani faifan bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna yadda masu zanga-zanga ke tserewa daga inda aka bude wuta da bindiga.

Yawan mutanen da abin ya rutsa da su na kara yawa tun bayan fara zanga-zangar. Wasu rahotannin sun nuna yadda wasu sojojin kasar ke rataya tutar kasar a kafada, alamun nuna goyon baya ga masu zanga-zanga.

Sai dai rahotanni na cewa wasu mutane sanye da bakaken kaya, wadanda suka rufe fuskokinsu, na ci gaba da bude wuta a kan masu zanga-zangar. Inda wani kaulin ke cewa 'yan bindiga ne masu goyon bayan kasar Iran.

Akwai sauran aiki

Zanga-zangar Lebanon ta fara ne ranar 17 ga watan Oktoba, bayan da gwamnati ta bullo da biyan haraji kan taba sigari, da fetur, da kuma kira ta manhajar WhatsApp. An soke sabbin harajin, sai dai da alama an makara.

Duk da cewar zanga-zangar ta Lebanon ba ta yi tsanani ba, amma an samu barkewar rikici a wurare daban-daban.

To ko juyin-juya-halin Larabawa ya dawo ne? Wannan alamu ne na cewa sauran aikin da ba a kammala ba ne tun 2011.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Guguwar juyin-juya hali ta kifar da gwamnatocin kasashe da dama na Larabawa shekara takwas da suka gabata

Tashin-tashinar da aka samu a shekarar (2011) ba ta samar da 'yancin da masu adawa da mulkin murdiya suka yi kokarin ganin an samu ba.

Sai dai har yanzu ana ganin tasirin tashin-tashinar, daga ciki akwai yakin Syria, da na Yemen, da kuma Libya, sai kuma na kasar Masar.

Sannan kuma har yanzu ba a magance koke-koken da masu zanga-zangar shekarar 2011 suke yi ba.

Gazawar gwamnatoci na biyan bukatun da yawa daga cikin al'ummarsu ta sanya har yanzu bukatun da masu zanga-zangar suka gabatar na nan a zukatan al'umma.