Wata bakuwar cuta ta kashe mutum 18 a jihar Katsina

Taswira

Har kawo yanzu ba a iya tantance kowace irin cuta ce ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 18 a kauyuka uku na karamar hukumar Matazu da ke jihar Katsina ba.

Jami'i mai kula da shirin lafiya a matakin farko na karamar hukumar, Abdulsalam Umar Jikamshi ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu dai mutum 45 ne suka kamu da cutar, inda 18 kuma suka mutu.

Abdussalam Jikamshi ya kara da cewa "wadanda da suka kamu da cutar sun yi fama da zazzabi da ciwon kai da amai."

Ya kuma kara da cewa tuni gwamnatin jiha ta aike da samfirin cutar zuwa birnin Legas domin yin gwaji wajen gano cutar da ke kisan mutanen.

Duk da cewa har yanzu ba a fahimci cutar da ke mamaya a karamar hukumar ba, Abdussalam Jikamshi ya ce ibtila'in ba zai rasa nasaba da rashin ruwan sha mai kyau da rashin kyawun muhalli da yankunan ke fama da su.

To sai dai wasu rahotanni na cewa adadin mutanen da suka mutu ya fi 18.

Amma Shugaban karamar hukumar ta Matazu, Kabir Faruk Matazu ya shaida wa BBC cewa "rahotannin da muke samu daga kauyuka abin babu dadi. Ba za mu iya tantance hakikanin mutanen da suka mutu ko kamu da cutar ba."

"Kasancewar wasu ba sa zuwa asibiti sannan wasu na tafiya wurin masu maganin gargajiya ya sa muke la'akari da kididdigar mutanen da suka zo asibiti."

Daga karshe shugaban karamar hukumar ya ce gwamnatin jiha na iya bakin kokarinta wajen ganin ta dakile cutar daga bazuwa.