Frank Lampard: 'Ina goyon bayan bai wa kananan 'yan wasa dama'

Mason Mount, Frank Lampard and Tammy Abraham

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mason Mount da Tammy Abraham duk kocin Ingila Gareth Southgate ya sanya su a tawagarsa

Frank Lampard ya ce yana yawan bai wa kananan 'yan wasa a Chelsea dama a kakar bana - koda kuwa kungiyarsa ba'a haramta mata sayen 'yan wasa ba.

A karkashin jagorancin Lampard, kungiyar tana yawan amfani da dan wasan gaba Tammy Abraham da dan wasan tsakiya Mason Mount da kuma dan wasan baya Fikayo Tomori.

"Ina yin hakan ne don na gwada iyawarsu," in ji kocin.

"Ko ba'a haramta mana sayen sabbin 'yan wasa ba, ina goyon bayan bai wa kananan 'yan wasa dama."

Lampard, mai shekara 41, ya kulla yarjejeniyar shekara uku a watan Yuli a daidai lokacin da aka dakatar da kungiyar daga sayen sabbin 'yan wasa har zuwa watan Janairun shekarar 2020.

Abraham da Mount sun ci wa Chelsea kwallo 12 a gasar firimiya kuma yanzu tana mataki na hudu bayan buga wasanni 10.

Kuma za ta kara da Manchester United a Gasar Carabao a ranar Laraba.