'Yan bindiga sun kashe sojoji 12 a Nijar

Sojoji

Wata sanarwa daga gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ce dakarun sojojin kasar 12 ne suka mutu yayin da wasu karin 8 suka yi rauni sakamakon wani hari da aka kai wa sojin a wani sansaninsu.

Gwamnatin kasar ta bakin Firai minista Briji Rafini ta kuma ta bayyana alhininta da mika ta'aziya ga al'umma kasar baki daya dangane da wannan 'babban rashi'.

Rafini ya ce maharan sun kai wa sansanin soji ne masu aikin kare kan iyakar kasar da kasar Chadi, da ke garin Gingime.

Wani jami'i a garin na Diffa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa 'yan bindigar sun kone kayan yakin sojoji sannan kuma sojojin ba su iya samun damar dakile harin ba.

Sai dai gwamnatin Niger ta ce maharan sun kwashi kashinsu a hannu, inda kuma har kawo yanzu sojojin na ci gaba da neman maharan.

A baya-bayan nan dai 'yan kungiyar Boko Haram sun sha kai wa yankin Diffa da ke jamhuriyar Niger hare-hare.