'Wasu tsiraru ne ke juya akalar fannin shari'ar Najeriya'

Atiku and Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 na jam'iyyar adawa ta PDP, Ahaji Atiku Abubakar ya caccaki fannin shari'ar kasar, bayan da kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da ya shigar a gabanta yana kalubalantar nasarar da ya samu a zaben watan Fabrairun 2019.

A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku Abubakar ya nuna shakku kan sahihancin fannin shari'a a Najeriya duk kuwa da cewa ya ce ya mayar da wukarsa kube ta neman hakkinsa kan zaben.

Ya ce fannin shari'ar Najeriya kamar kowane fanni na fuskantar zagon kasa daga wasu tsirarun mutane masu hana ruwa gudu wadanda suka mayar da hannun agogo baya.

A ranar Laraba ne dai alkalan Kotun Kolin kasar suka yi watsi da daukaka karar bisa dalilan rashin makama, inda kuma suka ce nan gaba za su bayar da dalilan da suka dogara da su.

A ranar Laraba ne dai alkalan Kotun Kolin suka yi watsi da daukaka karar bisa dalilan rashin makama, inda kuma suka ce nan gaba za su bayar da dalilan da suka dogara da su.

Tuni dai Atiku Abubakar ya amsa cewa damar da yake da ita, domin bin kadin zabe a gaban kotu, ta riga ta kare.

Ya ce hukuncin, wani bangare ne na kalubalen dimokradiyya, wanda ya zama dole su tunkara a matsayinsu na kasa.

Atiku Abubakar ya ce hanyar shari'a da ya dauka duk da cewa ta zo karshe, a saboda haka duk wata dama da yake da ita ta kare.

Atiku ya kuma ce an yi adalci a hukuncin ko ba a yi ba alkalanci ya rage wa 'yan Najeriya inda ya ce a amatsayinsa na wanda ya yi imani da tsarin demokradiyya ya yi fafutuka domin al'ummar Najeriya, kuma zai ci gaba da wannan fafutuka domin tabbatar da dorewar dimokradiyya da wanzuwar adalci,

Ya kara da cewa a tsarin dimokradiyya ana bukatar bangaren shari'a mai karfi da sakar wa 'yan jaridu mara da kuma barin hukumar zabe ta yi aiki ba tare da fiifta wani bangare ba.

Sai dai Atiku ya ce a Najeriya babu ko daya daga cikin wadannan abubuwa da ya zayyana a yanzu haka.

Dan takarar na jam'iyyar PDP ya ce ya kamata nasarar dimokradiyya ta kasance 'mutum daya kuri'a daya' amma idan aka yi watsi da hakan to fa an kama hanyar balbalcewa.

A ranar 11 ga watan da ya gabata ne dai kotun sauraron kararrakin zabe ta yi watsi da karar da jam'iyyar ta PDP ta shigar ta neman a soke zaben na watan Fabrairu, al'amarin da ya sa Atikun da PDP suka daukaka kara a kotun koli.

Kotun sauraron kararrakin zaben dai ta ce ta yi watsi da karar jam'iyyar PDP ne bisa gaza gamsar da kotun kan korafe-korafensu da suka hada da tafka makudi a zaben shugaban kasa da kuma ikirarin cewa shugaba Buhari bai cancanci tsayawa takarar ba bisa rashin mallakar shedar kammala sakandare.

Har wa yau, alkalan kotun sun ce jam'iyyar PDP ta kasa tabbatar da shaidun da ke nuna ita ce ta lashe zaben na shugaban kasa.

Sakamakon zaben na watan Fabrairu dai ya nuna Shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben da kashi fiye da 56 cikin 100 na kuri'un da aka kada.