Masu cin shinkafa 'yar waje lalatacciya suke ci - Hameed Ali

Rice seller

Shugaban hukumar hana fasakauri ta Najeriya, Kanal Hameed Ali ya ce 'yan Najeriya masu rurumar son cin shinkafar 'yar waje na cin wani abinci ne da ya riga ya lalace kasancewar kwanakin da aka deba mata sun kare.

Hameed Ali ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin da yake ziyarar gani da ido a ofishin hukumar da birnin Fatakwal na jihar Rivers, inda ya shaida yadda aka lalata wasu kwantainonin shinkafa 'yar waje da aka yi fasakaurinta zuwa Najeriya.

Ya ce "muna cin shinkafa 'yar waje wadda ta lalace kuma da zarar ta jaza wa mana cutar kansa sai ido ya raina fata. Abun da suke yi shi ne sauya wa shinkafar buhu domin ka da masu saye su yi zargin hakan. Irin fa abincin da muke ci ke nan fa."

"Mu a hukumar kwastam ta Najeriya dole ne mu fadakar da 'yan kasa ta hanyar 'yan jaridu domin jama'a su san irin gubar da suke zuba wa a cikinsu."

A watan Agusta ne dai Najeriya ta rufe kan iyakokinta al'amarin da ya janyo karuwar farashin shinkafar da ma karancinta a kasuwannin cikin gidan kasar.

Shugaban hukumar ta kwastam ya ce rufe iyakokin kasar zai amfani 'yan kasar a nan gaba a saboda haka dole ne sai 'yan kasa sun sadaukar da rayuwarsu.

Gwamnatin dai ta ce ba za ta bude kan iyakokin ba har sai kasashe masu makwabtaka sun daina tallafa wa masu fasakauri.

Bayanan hoto,

A farkon makonnan hukumar kwastam ta kama shinkafa da tramadol na fiye da 2bn