Mutum 65 sun mutu a gobarar jirgin kasa a Pakistan

Burning carriages

Asalin hoton, Reuters

Akalla mutum 65 ne suka mutu yayin da wani jirgin kasa wanda ya tashi daga Karachi zuwa Rawalpindi ya kama da wuta.

Ministan sufurin jiragen kasa na kasar Pakistan, Sheikh Rashid Ahmed, ya ce wata tukunyar gas ce da wasu fasinjoji suka yi amfani da ita domin girka abincin karin kumallo ta haddasa wutar.

An hakikance cewa wutar ta ci tarago akalla uku na jirgin.

Jami'ai sun shaida wa kafafen watsa labaran cikin gida cewa mutanen da wutar ta shafa sun mutu ne a lokacin da suke kokarin tsalle domin tsira da ransu daga jirgin.

An kuma samu karin wasu mutum 39 da suka jikkata sannan akwai hasashen alkaluman mutanen da suka mutu ka iya karuwa, kamar yadda wani jami'i ya shaida wa BBC Urdu.

An dai ce fasinjoji na da al'adar shiga jirgin da rusho da tukunyar gas domin shirya karin kumallo a lokacin doguwar tafiya, a fadin kasar ta Pakistan.

Asalin hoton, AFP/Getty