Rufe iyakan Najeriya don shinkafa ya bar baya da kura

Wani dan Najeriya tsaye kusa da shinkafar da yake sayarwa a kasuwar Ajara da ke Badagry, kusa da Lagos, ranar 6 Satumba 2019

Asalin hoton, AFP

Yanzu wata biyu ke nan da Najeriya, daya daga cikin manyan kashen Afirka ta rufe dukkan iyakokinta na kan tudu domin dakile ayyukan fasa-kwauri. Sai dai kuma matakin wanda ba'a taba ganin irin sa ba, na kawo cikas ga harkokin kasuwanci a yankin.

Iyakokin kasar wadanda a baya suke cike da hada-hada, yanzu sun tsaya cik. Baya ga kayayyaki da ke rubewa da dogon layin manyan motoci a shingayen bincike da ke jiran a sake bude iyakokin kasar.

A ranar 21 ga watan Agusta ne Najeriya ta rufe iyakokinta na kan tudu ba tare da wani gargadi ba - abin da ya fusata kasashe masu makwabtaka da ita.

Me ya sa aka dauki matakin?

Babban abin da ya sa Najeriya ta dauki matakin shi ne shinkafa. Kasar na takaicin yadda ake ta karya dokar da ta sanya na haramta shigo da shinkafa ta iyakonkinta na kan tudu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shinkafa ba ta fiye gundurar 'yan Najeriya ba - musamman girkin dafa-duka

Masu fasa-kwaurin shinkafa daga Jamhuriyar Benin na samun riba sosai.

Babbar haramtacciyar hanyar da suke bi na tsakanin Cotonou, birni mafi girma a Jamhuriyar Benin da kuma Legas, babban birnin kasuwancin Najeriya, mai nisan tafiyar 'yan sa'o'i.

Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Jamhuriyar Benin ya dogara ne sosai a kan sake fitar da kaya da harkar fiton kayan zuwa Najeriya. Bangaren na samar da kusan kashi 20 na kudaden shigar kasar.

Bankin ya kara da cewa kashi 80 na kayan da ake shigar da su Jamhuriyar Benin, akan saye su ne domin kaiwa Najeriya.

A 2004 Najeriya ta haramta shigar da shinkafa daga Jamhuriyar Benin, kafin a 2016 ta haramta shigo da shinkafar daga dukkan sauran makwabtanta. Amma duk da haka ba'a daina shigo da shinkafa kasar daga ketare ba.

Me ya sa shinkafa ke da riba sosai?

Ta tashoshin ruwa ne kadai Najeriya ta amince a shigo da shinkafa kasar. Tun a 2013 kasar ta sanya harajin kashi 70% a kan shinkafar da aka shigo da ita ta tashoshin ruwan.

Manufar matakin shi ne ba wa manoman shinkafa a kasar kwarin gwiwa, baya ga neman kara yawan kudaden shiga.

Sai dai kuma 'yan fasa-kwauri na amfani da damar saukin shigowa da shinkafa ta kasashe masu makwaftaka.

Shafin harkar teku ta Najeriya 'Ships and Ports' ya ce a 2014 Jamhuriyar Benin ta rage harajin da take karba a kan shinkafar dake shiga kasar daga kashi 35 na farashin da aka saye ta zuwa kashi 7. Ita kuma kamaru ta soke harajin kashi 10 da take karba a kan shinkafa 'yar waje.

Rice import from Thailand (metric tonnes). . Rice imports in selected African countries .

Sakamakon haka Jamhuriyar Benin ta samu karuwar shigowar shinkafa daga Thailand wadda ita ce kasa ta biyu da ta fi noma shinkafa a duniya.

Kusan kowane dan Jamhuriyar Benin mai mutum mililyan 11.5 zai iya cin kilogram 150 na shinkafa 'yar Thailand.

Da alamun cewa shinkafar na samun shiga Najeriya domin cike gibin da ake da shi a cikin kasar mai al'ummar da yawansu ya kai miliyan 200.

Kuma ana iya cewa 'yan Najeriya ba su gajiya da cin shinkafa wadda ta zama abincin yau da kullum a kasar.

A baya an taba samun lokacin da ake wa shinkafar kallon abincin alfarma, wadda sai a lokacin bukuwa ake ci. Amma yanzu saukinta, da kuma yadda 'yan kasar ke sha'awar girkin shinkafa dafa-duka ya sa ta zama kusan abincin duk 'yan kasar.

Shinkafa ce kadai kuwa?

Baya ga batun shinkafa, Jamhuriyar Benin ita ce babbar hanyar da ake shigar da gwanjon motoci zuwa Najeriya, wadda ta haramta shigar da motocin da suka yi fiye da shekara 15 da kerewa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Man fetur din da ke zuwa daga Najeriya ya fi sauki saboda tallafin gwamnati. Ana fasa-kwaurin man fetur din Najeriya domin sayarwa a Jamhuriyar Benin

Samun alkaluman gwamnati na da wuya, amma kamfanin jiragen ruwa na BIM e-solution da ke Luxembourg ya ce a kowane wata ana sauke mota kimanin 10,000 a Cotonou.

Hukumar kwastama ta Najeriya ta ce yawancin motocin ana shigowa da su cikin kasar ne ta barauniyar hanyan.

Hukumomin Najeriya kuma na kokarin dakile ayyukan sauran masu fasa-kwauri da ke daukar man fetur din da gwamnatin kasar ke biyan tallafi a kai suna sayarwa a kasashe masu makwabtaka da ita.

Price of petrol $. Selected African countries. Price of petrol in selected African countries As at 14 October 2019.

A watan Yuli, shugaban kamfanin mai na NNPC Maikanti Baru ya ce masu fasa-kwaurin mai na fitar da kimanin lita miliyan 10 na mai daga kasar a kowace rana.

Wane tasiri ya yi a Yammacin Afirka?

Wannan matsalar ta yadu inda ta shafi makwaftan Najeriya mafiya kusanci, wadanda suka hada da Jamhuriyar Benin da Nijar da Chadi da Kamaru da Ghana da Togo.

'Yan kasuwa a Ghana sun tafka asara mai yawa saboda an tsare kayansu na tsawon makonnin a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin, a cewar Ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey.

Minitstar ta shawarci gwamnatin Najeriya ta "nemo hanyoyin bambace matsalolin da kuma kasashen da take da matsala da su, domin kayan da ke fita daga Ghana su samu isa kasuwannin Najeriya ba tare da an yi musu kudin goro a wannan matsalar da aka samu ba".

Wani mai daukar hoto a Jamhuriyar Benin mai suna Yanick Folly ya wallafa hotunan wasu kwandunan tumatir da aka jejjera da ke ta rubewa a kusa da iyakar kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yanick Folly wani mai daukar hoto ne da ya wallafa hotunan tumatur da ke rubewa a iyakar kasar Benin

A ziyarar da ya kai wasu kasuwanni a garin Grand Pop, ministan gona na kasar Jamhuriyar Benin ya ce abin da ya gani abin damuwa ne matuka.

"Yana da matukar daure kai, wannan bala'i ne," kamar yadda kamfanin dillacin labaru ta ambato shi yana cewa.

Ita ma Jamhuriyar Nijar ta haramta fitar da shinkafa daga kasar zuwa Najeriya, a wani yunkuri na lallashin makwafciyar tata.

Sai dai wadanda abin ya fi shafa su ne al'ummomin da ke kan iyakoki inda 'yan kasuwa ke kai-komo wajen gudanar da harkokinsu.

Wakiliyar BBC Hausa a Jamhuriyar Nijar, Tchima Illa Issoufou ta ce harkokin kasuwanci sun tsaya a wasu yankuna biyu da ke kan iyaka da ta ziyarta saboda 'yan kasuwan yankunan ba su iya tsallaka iyakar.

Manyan motoci, yawancinsu makare da kaya sun yi wani dogon layi a yankin Maradi da ke kusa da Najeriya.

Shin Matakin ya saba doka?

Rufe iyakar ya saba wa yarjejeniyar da ta bayar da damar zirga-zirgar kaya a tsakanin kasa 15 na kungiyar tattalin arzikin Yammacin Afirka (Ecowas).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Iyakar Jamhuriyar Benin shi ne wurin da 'yan Najeriya masu neman gwanjon motoci suka fi tsallakawa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Duk da haka ya halastsa ga wata daga cikin kasashen Ecowas ta iyakance shigowar wasu kayan abinci da albakacin gona cikin kasarta. A 2014 Jamhuriyar Benin da Najeriya suka amince da haramta fitar da wasu kaya 29 na kasashen ketare zuwa Najeriyar.

Amma duk da haka akwai alamar tambaya game da yadda Najeriya ke kiyaye ka'idojin yarjejeniyar kasuwar bai-daya ta nahiyar Afirka, wadda ta rattaba hannu a kai a watan Yuli. An kulla yarjejeniyar AfCTA wadda ake gani a matsayin ginshikin kafa tsarin kasuwanci na bai-daya a duniya da nufin bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka.

Akwai masu ganin dabi'ar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na neman kare masana'antun kasar daga kasashe ketare ta yi daidai da abin da shugaba Amurka Donald Trump ke yi.

Wani mai sharhi kan harkokin kudi a Legas, Kalu Aja, ya ce rattaba hannu da Buhari ya yi a kan yarjejeniyar ya zama hujja a matsayin abin da ke bambanta Buhari da Trump.

Ya shaida wa BBC cewa "Ba kare masana'antun Najeriya daga na ketare Buhari ke yi ba. Neman ya kare ribar da bangaren noma na cikin kasar ke samu yake yi - musmman bangaren noman shinkafa.

"Kar a manta cewa har yanzu iyakokin ruwa na bude kuma ba'a kara haraji ba. Amma Trump ya rage haraji sannan ya sassauta wasu doka amma kuma ya sanya wa China da Canada karin haraji."

Me hakan ya yi wa Najeriya?

A jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya, wasu 'yan kasuwa masu harkar shinkafa a kasuwar Mile 1 da ke birnin Fatakwal sun rufe shagunansu.

Bayanan hoto,

Kasuwar da ke garin Fatakwal ta shahara a hada-hadar kasuwancin shinkafa

Sun ce rufe iyakokin kasar da aka yi ba zato, ba tsammani bai ba su damar kara sayo kaya ba.

Farashin kayan kuma ya tashi. Yanzu kudin shinkafa 'yar waje ya karu da kashi 60, farashin 'yar gida kuma ya karu, ya kusa ninkawa.

Amma akwai alfano.

A kwanan nan shugaban hukumar kwastam ta Najeriya Hameed Ali ya shaida wa 'yan majalisar kasar cewa kudaden shigan da ake samu sun karu domin yanzu kayan da za a kai Jamhuriyar Benin na sauka ne a tashoshin ruwan Najeriya.

A rana daya a cikin watan Satumba hukumar ta karbi harajin naira biliyan 9.2 (kimanin dala miliyan 25 - Fam miliyan 20), wanda ba'a taba samun haka ba a tarihi.

"Daga lokacin da aka rufe iyakokin mukan karbi harajin Naira biliyan 4.7 zuwa biliyan 5.8 a kullum, wanda a baya ba a samun ko kusa da hakan."

Yanzu me zai faru?

Ba wanda ya san abin da zai faru nan gaba. Kasar ba ta fadi ko zuwa yaushe za ta ci gaba da rufe iyakokin nata ga harkokin kasuwanci ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari da takwarans na Jamhuriyar Benin Patrice Talon sun kasa shawo kan matsalar a watan Agusta

A wani taro da aka yi a Japan a watan Agusta, shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon ya roki takwaransa na Najeriya ya sake bude iyakokin kasar, yana mai cewa "Mutanenmu na cikin wahala."

Sai dai kuma an ambato shugaban hukumar kwastam ta Najeriya na cewa iyakokin kasar za su ci gaba da zama a rufe, inda yake zargin kasashe makwaftaka da rashin katabus wurin yaki da ayyukan fasa-kwauri.

Wasu na zargin matsalar karbar rashawa da jami'an Najeriya da na makwaftanta ke yi a kan iyakokin kasar a matsayin babban abin da ke taimaka wa ayyukan fasa-kwauri.

Amma duk da haka, da alamun iyakokin Najeriya na iya cigaba da zama a rufe na wani lokaci kasancewar matakin bai shafi bangaren danyen mai da kasar ke fitarwa kasuwannin duniya ba.