Saudiyya ta shirya yin wasan kokawa na mata a karon farko

WWE promotional image showing Lacey Evans and Natalya

Asalin hoton, WWE

Za a gudanar da wasan restilin na mata a karon farko a Saudiyya ranar Alhamis, a lokacin da kasar ke daukar matakan sassauta dokokinta masu tsauri kan nishadi.

Wasan, wanda za a yi a Riyadh, zai kunshi taurarin wasan WWE Natalya da Lacey Evans.

Babu wani bayani kan ko masu wasan za su rufe jikinsu kamar yadda sauran masu yawon bude ido ke yi a baya.

Saudiyya ta yi kokarin ta sauya irin kallon da ake yi mata a duniya na wadda ta ke tauye hakkin mata ta hanyar kawo sauye-sauye a al'amuranta.

Gwamnatin ta dage haramta wa mata tuki a shekarar 2018 kuma ta sauya tsarin amfani da muharrami a kowane bangare na rayuwar mace a kasar a watan Agusta, kuma hakan ya bai wa mata damar yin fasfo da yin tafiya ba tare da izini ba.

Sai dai har yanzu mata na fuskantar matsi a rayuwarsu kuma an sha kama masu fafutukar kwato hakkin mata da yawa da ke kamfe a kan matsin.

Wasu daga cikinsu sun yi zargin cewa an azabtar da su a gidan yari.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Tsohon dan wasan dambe Tyson fury zai halarci taron na WWE Crown Jewel

Wasan na ranar Alhamis, na cikin taron WWE Crown Jewel da za a yi a filin wasa na King Fahd da ke Riyadh, wanda ke daukar 'yan kallo 68,000.

"Lokacin da na shiga WWE, burina shi ne in kawo sauyi a duniya da sauran mutane, kuma muna yin haka dai-dai gwargwado," in ji Lacey Evans.

Natalya ta ce: "Duk duniya za ta kalli wannan wasa. Ina matukar alfahari da wakiltar bangarenmu na mata."

Dan wasan damben Saudiyya Mansoor, wanda zai fafata da Cesaro ya shaida wa WWE.COM cewa 'yan uwansa mata da yawa sun kagu su kalli wasan a zahiri.

"Ba zan iya bayyana yadda nake ji ba a yanzu, musamman kannaina mata da ke son WWE da 'ya'yan 'yan uwana da kullum tunaninsu shi ne su zama 'yan dambe," a cewarsa.

Mansoor ya kara da cewa: "A lokacin da na fara... mutane da yawa kan tambaye ni, 'Shin kana ganin ko mata za su taba fafatawa a nan?'

"Nakan ce, 'kwarai kuwa', saboda lokacin da na girma, batun maza da mata su zauna a wuri daya abu ne da ba a taba ji ba. Yanzu mata na tuka mota. Sauye-sauyen da aka samu a kasar nan , duk lokacin da na zo sai in ga sun karu. Ina matukar alfaharin kasancewa ta a nan."