Najeriya ta dage haramci kan kungiyoyin agaji

Nigeria

Gwamnatin Najeriya ta ce ta dage haramta ayyukan kungiyoyin agaji guda biyu da ta yi a baya da suka hada da Action Against Hunger da Mercy Corps tun watan Satumba.

Yanzu haka an kyale kungiyoyin su ci gaba da gudanar da ayyuka amma na wucin gadi. An dai zargi kungiyoyin ne da taimaka wa mayakan Boko Haram.

Ministar jinkai, Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana haka a Abuja.

Akwai fargabar cewa akwai bukatar ayyukan jinkai a yankin arewa maso gabas, inda kungiyar Médécins Sans Frontières ta kiyasta cewa kaso 85 na yankunan jihar Borno na da wuyar shiga.

Gwamnatin ta ce yanzu za ta fara yi wa kungiyoyin na agaji masu aiki a yankin na arewa maso gabas rijista.

Kungiyar agaji ta Action Against Hunger dai ta ce a shirye take ta bayar da hadin kan da ya dace wajen gudanar da bincike sannan kuma ta musanta zargin cewa tana taimaka wa kungiyar 'yan ta'adda.