Majalisar Wakilan Amurka ta amince a fara shirin tsige Trump

Majalisar Wakilan Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An samu kuri'u 232 masu goyon bayan tsige Trump, inda suka rinjayi 196 wadanda ba sa goyon baya

Majalisar Wakilan Amurka ta kada kuri'a domin ci gaba da yunkurin tsige Shugaban Amurka Donald Trump.

Matakin da suka dauka zai ba da dama a bayyana cikakkun bayanai ga jama'a ba wai tsige shugaban kawai ba.

Kuri'ar wani mataki ne mai nuna samun goyon bayan tsige shugaban a majalisar wakilai wadda 'yan jam'iyyar Democrats ke da rinjaye.

'Yan jam'iyyar Democrats biyu ne kawai da duka 'yan jam'iyyar Republican ba su goyi bayan fara shirin tsigewar ba.

An samu kuri'u 232 masu goyon baya, inda suka rinjayi 196 wadanda ba su amince ba.

Ana dai zargin Mr Trump da matsa wa kasar Ukraine lamba a kan binciken rashawa da cin hanci da ake yi wa abokin hamayyarsa, Joe Biden da dansa wanda ya yi aiki a kamfanin gas na Ukraine, Burisma.

Mr Trump dai ya ki amince wa da aikata ba dai-dai ba inda kuma yake yawan bayyana yunkurin tsige shi da bita-da-kullin siyasa.