Julius Malema,: Kotu ta wanke jagoran 'yan adawa a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Jagoran 'yan adawa Julius Malema
Kotu a Afrika ta Kudu ta wanke jagoran 'yan adawa Julius Malema, bayan da wani minista ya maka shi kotu bisa zargin ya kira shi da 'karen farautar turawa 'yan jari hujja'.
Alkalin kotun Roland Sutherland ya yi watsi da karar da Mr Pravin Gordhan wanda minista ne a gwamnati mai ci ya shigar, inda kuma ya umarce shi da ya biya Mista Malema wasu kudade.
Ba wannan ne karon farko ba da ake samun takun saka da jagoran na jam'iyyar Economic Freedom Fighters.
A cewar Alkali Roland, kalaman na Mista Malema ba su zama barazana ba ga wanda ya yi karar ko kuma ga wani mutum ba.
Sakataren jam'iyyar EFF Godrich Gardee ya yi maraba da hukuncin, inda ya ce a matsayin su na yan jam'iyyar adawa, su na da 'yancin fadin albarkacin bakinsu.
Dama Mista Malema na zargin Mista Gordhan da yi ma sa bita-da-kulli kan dambarwa da ke faruwa tsakaninsa da hukumomin haraji, a lokacin da Mr Gordhan din ya ke rike da mukamin ministan kudin kasar.