Man United na bukatar Martinez, Edinson Cavani da PSG za ta bare?

Jurgen Klopp

Asalin hoton, AFP

Manchester City na cikin jerin kungiyoyin da ke neman dan wasan gaba na Steaua Bucharest da kasar Romania mai suna Florinel Coman kuma mai shekara 21. (Mail)

Manchester United kuwa na son sayen Lautaro Martinez, dan kasar Argentina mai shekara 22 daga Inter Milan a kan euro 111. (Mundo Deportivo ta Sfaniyanci)

Roma na gaf da kammala sayen Chris Smalling kan fam miliyan 18. Dan wasan mai shekara 29, ya koma can ne bayan da Manchester United ta bayar da aronsa na tsawon kakar wasa guda. (Corriere dello Sport)

Kungiyar Liverpool na duba yiwuwar tura kungiyoyi biyu a gasa biyu da aka shirya cewa za ta buga a rana guda. Gasa ta farko ita ce ta Carabao wanda za ta buga da Aston Villa, sannan za ta buga wasa a gasar Kungiyoyin Duniya da FIFA ke shiryawa. (Mirror)

Crystal Palace na cikin kungiyoyin da ke son karbar aron dan wasan gaba na Liverpool mai shekara 19, wato Rhian Brewster. (Sun)

Inter Milan na bibiyar lamarin Matteo Darmian mai shekara 29, wanda dan wasan baya na Parma ne ko zai iya komawa can nan ba da dadewa ba. (Gazzetta dello Sport)

Edinson Cavani dan kasar Uruguay ya bayyana cewa ba ya jin dadin halin da yake ciki a Paris St-Germain. Kocin kungiyar, Thomas Tuchel, wanda ya ajiye dan wasan mai shekara 32 a bisa benci ne ya bayyana haka. (Le Parisien)