Wuta ta yi barna a kasuwar waya ta Maiduguri

Fire fighters dey quench di fire Hakkin mallakar hoto Isyaku Yau

An dai ce gobarar wadda ta fara da yammacin ranar Alhamis ta kai cikin daren Juma'a tana ci inda kuma ta yi wa shaguna 47 kurmus na kasuwar wayar ta Jagwal da ke birnin Maiduguri.

Wani jami'in hukumar kashe gobara ta jihar ta Borno, Ali Kanti ya shaida wa sashen BBC na Pidgin cewa jami'ansu sun samu nasarar kashe wutar ne da misalin karfe daya na daren Juma'a.

Ya ce " wutar ta fara ruruwa ne da misalin karfe 8:47 na daren Alhamis inda jami'anmu suka garzaya zuwa kasuwar domin kai dauki kuma da misalin karfe 1:15 na dare muka kashe ta."

"To sai dai yanzu da nake magana da ku, jami'anmu wadanda suka kwana a kasuwar ba su dawo ba saboda haka sai yau din nan za mu iya tantance irin asarar da wutar ta janyo."

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun wuta irin wannan da ke barna a kasuwar domin an taba samu a 2015, inda ta kone shaguna 14 abin da da ya yi sanadiyyar asarar miliyoyin kudi.