Mai hukunta mazinata ya sha bulala kan zina

Aceh Ulema Hakkin mallakar hoto AFP

Wani mutum dan Indonesiya- wanda ya yi aiki da hukumar da ta rubuta daftarin dokokin zina masu tsauri ya sha bulala a bainar jama'a bayan da aka kama shi yana aikata zina da wata matar aure.

An yi wa Mukhlis bin Muhammad na kungiyar malamai ta Aceh Ulema Council (MPU) bulalala 28.

Matar da ya aikata zinar da ita ta sha bulala 23.

Mukhlis ya fito ne daga yankin Aceh mai tsattsauran ra'ayin addini, wani wuri guda a Indonesia da ke aiki da Shari'a.

Ana hukunta 'yan luwadi da 'yan caca ta hanyar yi masu bulala.

"Wadannan dokokin Allah ne. Duk wanda aka kama da laifi dole ne a hukunta shi ko da dan kungiyar MPU ne," in ji Husaini Wahab, mataimakin magajin garin Aceh Besar, inda Mukhlis ya ke zaune.

Jami'ai sun kama mutumin da matar ne a watan Satumba, a cikin wata mota da aka ajiye a wani wurin shakatawa na bakin ruwa.

An yi masu bulalar ne ranar Alhamis. Mista Husaini ya kara da cewa za a kori Mukhlis daga MPU .

Mukhlis ne shugaban addini na farko da aka taba yi wa bulala a bainar jama'a a Aceh tun da aka fara aiki da dokokin Shari'a a 2005.

Labarai masu alaka