'Yan sanda sun kama Fasto mai gidan mari a Najeriya

Mari

'Yan sanda a jihar Legas sun ceto mutum 15 da suka kasance cikin mari da sarka a wani gidan mari da wani fasto da ke ikirarin annabta ke gudanarwa a unguwar Ijegun a birnin.

An dai samu nasarar ceto mutanen ne tare da cafke faston bayan da 'yan sanda suka kai wani samame ranar Laraba sakamakon samun labari da suka yi.

Mutanen 15 wadanda suka hada mata da maza masu shekaru 15 zuwa 19, sun shaida wa hukumomi cewa sun shafe shekaru fiye da biyar a kulle a gidan faston.

Mahaifan matasan ne dai suka kai su gidan fasto domin nema musu maganin matsalar tabin hankali da sauran nau'in cututtuka.

Mai gidan marin, Sunday Joseph Ojo ya ce tun shekarar 1986 yake tafiyar da gidan domin sama wa jama'a waraka.

Wannan ne dai karon farko da a baya-bayan nan aka kai wa gidan mari a kudancin Najeriya samame.

Za a iya cewa an fi samun irin wadannan gidaje a arewacin kasar, inda a watan nan kadai an kai samame kan gidajen fiye da biyar a bangarori da dama na yankin.

Sai dai masu gidajen na mari na cewa suna gyara halayyar matasan da suka kangare ne.

A Najeriya dai akwai karancin cibiyoyin gyara halayyar jama'a mallakar gwamnati. al'amarin da ya sa wasu ke ganin shi ne dalilin da ya sa ake yawan samun gidajen mari a fadin kasar.