Malaman jami'o'in Najeriya sun ki amincewa da tsarin biyan albashin bai-daya

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya wato ASUU, ta ce ba za ta amince da tsarin biyan albashin bai-daya (IPPIS) da gwamnatin tarayyar kasar ta fito da shi ba, sakamakon cin karo da dokar da ta kafa jami'o'in kasar.

Shugaban kungiyar malam jami'o'in reshen Jami'ar Bayero da ke Kano, Farfesa Ibrahim Garba ne ya bayyana hakan gabannin taron kugiyar na shiyar arewa maso yammacin Najeriya, da ke gudana a sakatariyar kungiyar da ke Jami'ar ta Bayero.

Gwamnatin Najeriyar ta samar da tsarin biyan albashi na bai-daya ne a karkashin ofishin babban akantan kasar domin ganin an biya dukkan ma'aikatan gwamnatin albashinsu kai-tsaye zuwa asusun ajiyarsu na bankuna, tare da sanya idanu kan yadda ake cirar kudin ma'aikatan kasar.

A yayin tattaunawar, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana cewa tsarin albashin na bai-daya bai dace da jami'o'in kasar ba, shi yasa suka shirya taron domin yin shawarar matakin da ya kamata su dauka domin sanar da uwar kungiyarsu, kafin daukan mataki na gaba.

A kwanakin baya ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin biyan albashi ga duka ma'aikatan gwamnati ta tsarin bai-daya wato IPPIS.

Shugaban ya bayyana cewa duk wani ma'aikaci da ba shi a kan tsarin daga 31 ga watan Oktoba ba zai samu albashinsa ba.

Labarai masu alaka