Kalli wasu zababbun hotunan Afirka na wannan makon

Wasu daga cikin zababbun hotuna daga nahiyar Afirka da kuma 'yan Afirka a wasu sassa na duniya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daruruwan mutane ne suka samu mafaka a wannan cocin a Afirka ta Kudu, bayan korar su daga daga harabar ofishin hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta MDD inda suka shafe makonni uku suna zanga-zanga
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Talata, wani limami kenan ya ke bude kofar Masallaci a birnin Agadez mai dumbin tarihi na Jamhuriyyar Nijar.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wata mai yawon bude ido kenan a Cape Town da ke Afirka ta Kudu ta tsaya domin daukar ta hoto
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Asabar, mutane ne da dama suka yi wani tattaki na kungiyoyin 'yan luwadi da madigo a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tattakin an yi shi ne domin cika shekara 30 da 'yan kungiyoyin suka samu 'yanci
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan makarantar Firamare kenan ke rubuta jarabawa ta matakin karshe na gama firamare a birnin Nairobi da ke Kenya a ranar Talata.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu dalibai kenan ke zanga-zanga a wata jami'a da ke Uganda sakamakon kudirin da aka gabatar na karin kudin makaranta da kashi 15 cikin 100, an dauki wannan hoto ne a daidai lokacin da 'yan sanda suka harba musu hayaki mai sa hawaye.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan Zimbabwe sun yi wata zanga-zanga a ranar Juma'a sakamakon wani takunkumi da Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Amurka suka kakaba wa kasar.
Hakkin mallakar hoto NurPhoto
Image caption Wasu direbobin babbar mota kenan ke bacci a karkashin mota a birnin Legas da ke Najeriya.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC