Yadda ake fama da maleriya a unguwannin Abuja

Latsa alamar lasifika domin Sauraren rahoton Zaharadden Lawan:

Mazauna wasu unguwannin marasa galihu Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya sun koka game da karuwar yaduwar cututtuka saboda karancin ababen more rayuwa da rashin cibiyoyin kula da lafiya.

Wani rahoto da wata kungiya mai suna Do Inspire, da ke bayar da shawarwari kan kiwon lafiya ta fitar, ya nuna cewa ana samun karuwar kamuwa da zazzabin cizon sauro da kashi 20 cikin 100 a irin wadannan unguwanni.

Binciken ya nuna cewa ana samun kimanin mutum miliyan 100 da kan kamu da cutar maleriya, yayin da sama da 300,000 ke mutuwa kowace shekara sanadiyyar cutar a Najeriya. Wanda hakan ya zarta wadanda ke mutuwa sanadiyyar cutar HIV.

Zaharadden Lawan ya ziyarci daya daga cikin unguwannin na marasa galihu a Abuja kuma ya aiko da rahoto.