Yadda dillalai ke sanya gidaje tsada a Legas

Apartment in Lagos Hakkin mallakar hoto Gloria Yusuff

Samun matsugunni abu ne wanda yake damun matasa a wurare daban-daban. kuma matsalar ta fi kamari a Legas babban birnin kasuwanci na Najeriya.

Yawanci masu gidan haya sukan bukaci wanda ya karbi gidansu haya ya biya kudin shekara biyu zuwa uku baya ga kuma kudin dillali da kudin yarjejeniya.

A kan gida mai daki biyu wanda ke da wutar lantarki a kusa da tsakiyar gari Victoria Island, ana neman mutum ya bayar da tsakanin dala 11,000 zuwa dala 22,000 kafin kama gidan.

Gaba ki daya dai, matsakaicin gida ko gidan alfarma kan iya kai tsakanin dala 5,000 zuwa dala 40,000 a shekara.

Wadannan kudin mutane kadan ne ke da su.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai karancin dakunan da matasa za su iya kamawa.

Abin fahimta a kan kama gida mai tsada na zuwa ne daga tsadar gidan da inda filin yake da kuma tsadar gini a Legas.

Kuma akwai karancin kananan gidaje wadanda irin su ne mutane suka son kamawa haya.

Sabuwar hanyar kama haya

Tsarin biyan gidaje kafin a kama su na fifita masu gidajen haya, amma wasu masu aiki da fasaha na shirin fito da hanyar da za ta taimaki masu kama haya.

Bankole Oluwafemi, wani matashi dan kasuwa ya samu wani gida mai kyau a unguwar Lekki, wata unguwar masu kudi. Yana zaune ne tare da wasu matasa masu aiki su uku.

Wasu mutane na amfani da wasu hanyoyi da suke samun kudi daga iyayensu ko ajiye kudi a yayin da suke zama tare da 'yan uwansu. Wasu wuraren aiki kuma suna bai wa ma'aikata bashi.

Amma mista Oluwafemi ya samu wurin ne ta hanyar wani wurin da ake samun gidajen haya ta intanet mai suna Fibre.

Manhajar ta intanet na bai wa masu amfani da ita damar kama wuri ta hanya mai sauki.

Ana bai wa masu zama gidan hayar damar biyan kudi a karshen wata ko bayan watanni uku, wanda a wasu kasashen duniya ba abin a zo a gani ba ne, amma wannan wata hanya ce ta daban.

Dolapo Omidire
BBC
Landlords have the authority to dictate what they want from tenants"
Dolapo Omidire
Real estate analyst

Bayan da Mista Oluwafemi ya gama jami'a , sai ya tafi Legas a 2011 amma bai samu damar biyan kudin hayar na shekara biyu ba kafin ya shiga gidan ka,mar yadda mai gidan ya nema.

Rashin samun gidan ne a wuri mai kyau ya sanya shi kwana kasa a wani daki tare da mutum 10.

Daga baya da ya hada hannun suka kirkiri kamfani na fasaha sai ya yanke shawara da ya rika kwana a ofis domin kaucewa biyan kudin haya.

'Ba mu raina komai'

"Zama a Legas na bukatar ka da ka zauna a gidan haya, amma a wata mahangar dole ka zama karamar hukumar kanka domin ka sama wa kanka abubuwan more rayuwa" a cewar Mista Oluwafemi

Yana nufin cewa ban da kudin haya, ana tsammanin masu zama gidan haya su za su biya kudin ruwan shan su da wutar lantark, wadanda suna da tsada saboda man janareta.

"Fibre ba wai na zuwa ba ne da ikon biyan kudin a wata ba kawai, wadannan gidajen na zuwa da wani tsari na samun inganci mai kyau.

"Mutane na daukar wadannan abubuwan da rikon sakainar kashi a sauran wurare a duniya , amma mu muna zama ne a nan Najeriya."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Lagos landlords think single ladies are prostitutes'

Duk da cewa a shekarar 2011 gwamnatin Najeriya ta kafa doka a shekarar 2011 domin iyakance ikon masu gidajen haya kan amsar kudin haya na sama da shekara daya daga hannun masu zama a gidajen, dokar na neman zama mai wahala wajen aiwatarwa.

A cewar mai sharhi kan muhallin zama Dolapo Olumidire, Legas wani wuri ne na masu gidajen haya.

"SUna da ikon neman abin da suke so daga masu zama gidajen" a cewarsa.

"Za su iya cewa: 'Wadannan ne sharuddanna. Idan ba ka so ka tafi wani wuri.'"

Dogon layin jira

Demi Ademuson da Obinna Okwodu ne suka kafa Fibre shekara uku da suka wuce. Suna hada hannu da masu gidajen haya da magina domin bayar da gidaje masu kyau.

Saboda kokarin samar da sauki da yanayi mai rahusa ga masu neman gidajen haya, manhajar na kalubalantar tsarin da baya da sauki ga matasa.

Obinna Okwodu
BBC
It doesn't make sense that for something so fundamental you have to jump through so many hoops"
Obinna Okwodu
Fibre co-founder

"Wannan na yi wa mutane tsadar samun gida" a cewar Mista Okwodu.

"Saboda muhimmancin muhalli bai kamata a ce mutane suna wahala wurin neman wurin zama ba."

Da kastomomi 200 suna haya a gidajen da mutum 5000 suna jira a layi, Fibre na wakiltar wani bangaren kasuwar ne. Amma babu madadin wannan.

Sun ce sun aminta cewa sun fara ne da masu hali, amma za su fadada domin karin kastomomi.

Abin yana yi. Mista Okwodu ya ce da farko akwai kalubale sosai kafin suka shawo kan masu gidaje haya suka yarda su rika amsar kudin haya a wata wata.

Kamfanin ke daukar alhaki idan masu zama suka kasa biyan kudin hayar. Hakan ya sanya mutane sun kara yadda da tsarin.

Masu gidan haya na son tarin kudi

Masu gidajen haya da yawa ba su son ana biyan su kudin wata -wata.

Mai harkar gine ginan gidaje Deborah Nicol-Omeruah na gain cewa biyan kudin wata-wata zai taimaki masu gidajen, amma ita ta fi son tsarin da k akwai a yanzu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mazauna cikin gari na wahala kan hanyar su ta zuwa aiki

"Biyan kudin kadan kdan zai baka dama ka yi amfai da kudadenka kan wasu abubuwa. Misali kamar biyan kudin makaranta ko tafiya yawan bude ido"

Mafi muhimmanci a cewar Ms Nicol-Omeruah biyan kudin shekara kafin ta zo zai hana ka kasa biyan kudin haya.

"Idan ana biyanka wata-wata, za ka rika fama da su su biya. Idan ba za su iya biya ba za ka rika fama da su a kowanne wata.

"Amma a wanna tsarin na yanzu sau daya kawai za ka bi mai zama domin ya biya kudin."

Nasarar da Fibre ta samu ta karfafa wasu inda suka fito da wadannan manhajoji domin saukake halin da kasuwar ke ciki.

Mutane da yawa ba su da zabi, ko dau su zauna tare da wasu ko su zauna tare da 'yan uwansu.

'Awa takwas kan hanya'

Mai gabatar da labarai Uche Okoronkwo na zama tare da baffanta a wata unguwa da ake cikin gari a lokacin da ta fara zuwa Legas.

Amma tafiyar awa takwas daga gida zuwa ofis wurin aikinta a cikin gari inda kamfanoni da yawa suke na da wahalarwa.

Image caption Taswirar Legas

"Tafiya daga Mainland zuwa kan tsibiri azaba ce. Ina tashi da karfe hudu na asuba inda take hawa achaba domin ta je ta hau bas da karfe 04:30 domin ta isa wurin aiki da karfe takwas na safe.

"Ina komawa gida da karfe 10 ko 11 na dar. Saboda ba na barin Island da dare idan ba ka fita da wuri ba har hanya ta cunkushe. Ba za ka ci gaba a haka ba. Babu ingancin rayuwa.

Ms Okoronkwo ta hanke shawarar komawa Island amma saboda rashin muhalli sai ta kama wani "wurin maza" BQ wani wuri mai daki da kewaye wani wurin da ake aje 'yan aikatau.

"Wurin karami ne kuma babu dadi" a cewarta. "Bututun ruwan bai da kyau. Babu ruwa sai na saya kuma da janareta ne kawai za ka samu wutar lantarki".

Image caption Tsadar kudin gina gidaje kan kare kan masu kama haya

Babu wani tsari kan cinikayyar muhalli a cewar masani Mista Olumidire wanda ya ce kadan daga cikin masu gina gidaje ke son saka kudadensu domin tabbatar da inganci.

Duk da haka, yana farin cikin ana samun karuwar masu ginane gida mai daki daya ko biyu ba a ga matasa masu aiki.

Ya ce wannan zai magance karancin abin da mutane suke so da abin da ke akwai a kasuwa.

Sannan akwai kamfanoni irinsu Fibre wadanda ake kafawa a Najeriya, suna magance matsalar kama gidan haya.

Wadannan kafafen suna kananan aiki ne, amma idan sun girma za su iya sauya yadda ake kama haya ta hanyar samar da sauki wurin kama haya.

Labarai masu alaka