Nigeria ta ba da sharudda kafin ta bude iyakokinta

Nigeria Minister of foreign affairs Geoffrey Onyeama Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI
Image caption Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffery Onyeama

Gwamnatin Najeriya ta bai wa kasashen da ke kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta yamma, ECOWAS, wasu sharudda, wadanda ta ce dole su cika su, kafin ta bude bakin iyakokinta.

Tun a watan Agustan shekarar da ta wuce ne kasar ta rufe iyakokinta na kasa da suka hada ta da kasashen Chadi da Benin da Niger da kuma Kamaru.

Ministan harkokin wajen kasar, Geoffrey Onyeama, ya bayyana sharuddan wadanda suka shafi zirga zirgar mutane da kayayyaki ta bakin iyaka, a wajen wani taron kwamitin da ke sa ido kan rufe wasu iyakokin kasar da aka yi a Abuja.

Sharadin farko

Daya daga cikin sharuddan shi ne Najeriya ba zata yarda a dinga shigo da kayan da aka sauya musu mazubi ba a makwabtan kasashe.

Mista Onyeama, ya ce dole kasashen ECOWAS su mutunta dokar kungiyar, idan har suna so su shigar da kayayyaki kasar.

Kasar ta ce dole kuma a san daga inda kayan suka fito, idan daya daga kasashen kungiyar ne suka sarrafa ko kera kayayyakin, dole a nuna shaidar hakan.

Idan kuma kayayyakin an shigo da su ne daga wasu kasashen ketare to dole ya zamanto kashi 50 cikin dari na abun da aka kera ko sarrafa din, ya fito ne daga kasashen yankin Afrika ta yamma.

Haka kuma ya ce gwamnati za ta fitar da sharuddai na yadda ta ke son a dinga kunshe kayayyaki ko irin mazubin da ya kamata a zuba kayan da za a ketaro da su cikin kasar.

Sharadi na biyu

Abu na biyu kuma shi ne dole su rushe dukkanin wuraren ajiye kayayyakin da ke bakin iyaka ko kusa da iyakokin Najeriya.

"Daga yanzu ba za mu yarda a shigo mana da duk wani abun da bamu san shi ba ta bakin iyakokinmu. " A cewar ministan.

Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI
Image caption Wata biyu ke nan da rufe bakin iyakar Najeriya da Benin

Sharadi na uku

Shi ma wannan sharadin dole ne cewa a yi wa kayayyakin da za a shigo da su daga makwabtan kasashe rakiya.

Dole masu rakiyar su taso tare da kayayyakin tun daga wata tashar jiragen ruwa da ke yankin, kai tsaye zuwa bakin iyakar Najeriya.

Sharadi na hudu

Haka kuma mutanen da ke da fasfo ne kawai za a bari su ketaro cikin kasar.

Onyema ya yi gargadin cewa, kasar ba za ta amince da wata takarda ko katin shaidar zama dan kasa ba.

Nan da makonni biyu masu zuwa ne ake sa ran wani kwamiti wanda ya kunshi wakilai daga kasashen Benin da jamhuriyyar Niger da kuma Najeriyar zasu gana.

Ministocin kudi da na harkokin waje da na cikin gida da shugabannin hukumomin hana fasakauri da na shige da fice da hukumomin tattara bayanan sirri na kasashen ne za su yi wannan ganawar. In ji Mista Onyeama.

Labarai masu alaka