Oscar: Turanci ya janyo watsi da fim din 'yan kudancin Najeriya

Wadda ta ba ta umurnin shirya fim din, Genevieve Nnaji Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wadda ta ba ta umurnin shirya fim din, Genevieve Nnaji

Mai ba da umurnin shirya fina-finai kuma jaruma Genevieve Nnaji ta nuna rashin jin dadinta kan fitar da fim dinta Lionheart da Oscar ta yi.

Oscar ya fitar da fim din na barkwanci saboda "an yi amfani da harshen turanci sosai a ciki" wanda hakan ya saba wa sharadin shiga gasar fim mafi kyau na kasa da kasa domin an fi so a yi amfani da wani harshe ba turanci ba.

A fim din na Lionheart wanda shi ne na farko daga Najeriya wanda ya kai wannan mataki an yi amfani da turanci ne inda minti 11 ne kawai aka yi harshen Igbo.

Fim din wanda ya samu yabo ana nuna shi ne kan manhajar Netflix, an shirya kada kuri'ar a zaben sashen fim din kasa da kasa a ranar Laraba kafin aka fitar da shi.

An bayyana fitar da fim din daga gasar ga masu kada kuri'ar a ranar Litinin a cewar shafin The Wrap.

Fim din na daga cikin 29 cikin 93 wanda mata suka ba da umurnin shirya shi wanda aka gabatar domin neman cin gasar a wannan shekarar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Tattaunawa da Ibrahim Sheme

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron tattaunawar Muktar Adamu Bawa da Ibrahim Sheme

Kan wannnan lamari, BBC ta ji ta bakin wani mai sharhi kan fina-finai a Najeriya Ibrahim Sheme kuma ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka yi watsi da wannan fim din a gasar Oscar.

Ya shaida cewa lokacin da aka saka wannan fim a gasar Oscar, sun ji dadi matuka a wannan lokaci kuma ya ce ba su ga fim din da zai doke ''Lionheart'' ba cikin jerin fina-finan kasashen duniya.

Ya ce wannan mataki da aka dauka na cire fim din daga gasar ''cin fuska ne ga Najeriya.''

Ms Nnaji ta yi korafi kan korar fim din a shafinta na Twitter inda ta ce "Fim din na nuna yadda mu 'yan Najeriya ke yin magana"

Ta kara da cewa "wannan ya hada da turanci, wanda shi ne ke sada sama da harsuna 500 da ake magana da su a kasar. Ba mu muka zabi wadanda suka yi mana mulkin mallaka ba. To dai, wannan fim din da da yawa irinsa an yi su ne a Najeriya."

Babbar daraktar mai ba da umurni Ava DuVernay a shafinta na Twitter inda take tambaya idan fitar da fim din ba nufin "haramtawa" Najeriya har abada sake shiga gasar ta Oscar.

Harshen Turanci dai shi ne harshen da ake amfani da shi a matakin gwamnati a mafiya yawan kasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka a Afirka.