Abin da ya sa Facebook ya yi wa sunansa kwaskwarima

Facebook new and old logos Hakkin mallakar hoto Facebook

Kamfanin Facebook ya fito da wani sabon suna da zai dinga amfani da shi, a wani yunkuri na bambanta kamfanin da manhajarsa da kuma shafinsa na intanet.

Shafukan Instagram da WhatsApp na daga cikin abubuwan da za su fara amfani da sabon sunan na FACEBOOK nan da 'yan makonni masu zuwa.

Sai dai manhajar Facebook da kuma shafin intanet za su ci gaba da amfani da sunan da aka saba amfani da shi mai shudin launi.

Haka kuma sabon sunan da manyan baki, an rubuta shi ne da wani tsarin rubuta daban da na sauran abubuwan da kamfanin yake samarwa da kuma manhajarsa.

Sannan za a dinga rubuta sunan da launuka daban-daban wanda ya danganta da nau'in abun da yake wakilta. Ga misali kamfanin zai yi amfani da sunan da koren launi a kan WhatsApp.

Hakkin mallakar hoto Facebook

"Muna son sunan ya zamanto yana da alaka da duniya da kuma mutane," A cewar Facebook. "Tsarin sauyin launin zai kasance ya zo daidai da muhallin da yake."

Shugaban sashen tallace-tallace na Facebook, Antonio Lucio ya ce :

"Wannan sauyin wata hanya ce ta bayyana yadda tsarin mallaka ya ke a kamfanin ga mutane da kuma harkokin kasuwancin da ke amfani da abubuwan da muke samarwa. "

Sanata Elizabeth Warren ta Amurka ta ce tana son ganin an rarraba manyan kamfanonin fasaha kamar su Facebook da Amazon da kuma Google, sannan a sanya musu kwararan dokoki.

Facebook ya fuskanci suka kan wasu batutuwa a baya-bayan nan.

Shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg, ya bayyana a gaban 'yan majalisar Amurka a watan jiya domin yin bayani kan manufofin kamfanin kan tabbatar da gaskiyar abubuwan da ake tallatawa na siyasa.

Haka kuma ya kare shirin kamfanin na kudin intanet da gazawar da shafuka sada zumunta suka yi na hana cin zarafin yara. Haka kuma ya amsa tambayoyi kan abin kunyar nan na Cambridge Analytica da ya yi amfani da bayanan miliyoyin mutane ba tare da amincewarsu ba.

A farkon wannan shekarar ne, Mista Zuckerberg ya ce kamfanin zai yi wasu sauye-sauye a shafukan sada zumuntarsa don inganta abubuwan da suka shafi sirrin mutane.

Labarai masu alaka