'Yadda 'yan fashi ke hana mu barci a jihar Neja'

'Yan fashin sun yashe rumbunan abinci a garin
Image caption 'Yan fashin sun yashe rumbunan abinci a garin

Ya za ku yi yayin da kake tsaka da barci kawai sai ga bera ya diro daga silin dakinku yana neman mafaka daga harin 'yan fashi masu dauke da bindiga?

Wannan shi ne halin da al'ummar yankin Kompani Madaka na karamar hukumar Rafi da ke jihar Naija ke ciki a kusan kowace rana.

Har yanzu jama'ar yankin suna cikin alhinin wani hari da 'yan fashi suka kai masu ba, inda suka bi gida-gida dauke da bindigogi suna kwace masu "abin da suka yi shaekaru suna tarawa".

Har wa yau, suna cikin fargaba saboda rashin jami'an tsaron da za su kare su.

'Yan bindigar kan ci karensu babu babbaka ta yadda suke addabar kauyuka bakwai na yankin daya bayan daya. Sukan nemi a ba su kudi ko akuyoyi ko kayan abinci, har ma da tufafi.

Gwamnatin jihar Naija ta ce ta tura jami'an tsaro domin fatattakar 'yan fashin.

Sai dai mutanen yankin sun ce har yanzu ba su ga wani sauyi ba.

Image caption Isaac ya ce har yanzu jama'a na cikin alhinin harin

Isaac na cikin wadanda abin ya shafa a baya-bayan nan, 'yan fashin sun kwashe komai daga shagonsa. Ya ce har yanzu bai farfado ba daga fashin.

Mazauna kauyen sun shaida wa sashen Pidgin na BBC cewa 'yan fashin kan zo kauyen a babura sai su rarraba kan su zuwa rukunin mutum biyar-biyar sannan su far wa jama'a.

Wani mazaunin yankin Adamu Shehu, ya ce jama'ar kauyukan ba su da ta-cewa ko kadan. Ya ce a harin baya-bayan nan sun sace akalla saniya 30 da tunkiya 40 da kuma wayar hannu 40

"Bayan abin ya faru sojoji sun zo sun tafi amma kamar yadda kuke gani babu wani tsaro yanzu. Muna cikin zulumi a kodayaushe," in ji Adamu

Image caption Mutanen sun ce gwamnati ta yi watsi da rayuwarsu

Wata mai suna Aisha ta ce suna cikin fargabar fyade a matsayinsu da mata da kuma sace 'ya'yansu.

Sannan ta ce har yanzu babu wani tallafin tsaro da suka samu daga gwamnati.

Image caption Aisha ta ce sun sace masu duk abin da suka tara na tsawon shekaru

Shi kuma Oga Kayi Haasan cewa ya yi sun sace masa awakinsa baki daya, amma abin da ya fi damunsa shi mne na rashin jami'an tsaro a yankin.

Image caption Kayi Haasan ya ce sun sace masa awakinsa amma ya bar su da Allah

"Muna neman gwamnati da ta kula da rayuwarmu mu mazauna kauye. Mu muka zabe su amma sun yi watsi da mu bayan sun yi nasara," ya bayyana bacin ransa.

Me yasa kauyukan jihar Naija ke fuskantar hare-hare?

Tun a shekarar bara ne 'yan bindigar suka fara kai hare-hare a jihar Naija.

Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Matane ya ce wuraren da abin ya fi shafa su ne: Rafi da Moriga da Shiroro da kuma Wumya.

Hakan na faruwa ne saboda garuruwan sun yi iyaka da jihohin Zamfara da Kaduna da Kebbi, inda sojoji suke fatattakar 'yan fashi, abin da ya sa da damansu suke neman mafaka a dazukan jihar ta Naija kuma su yi wa jama'ar yankin fashi.

Image caption Gwamnnati ta rufe makarantu saboda matsalolin tsaron

Me jami'an tsaro ke yi?

A ranar Alhamis rundunar sojan Najeriya ta kaddamar da wani shirin fatattakar 'yan fashin mai lakabin Operation Cat Race.

An ce shirin zai kai har watan Disamba ana aiwatar da shi amma da wakilyar BBC ta sashen Pidgin ta ziyarci yankin babu wata alamar jami'an tsaro.

Ibrahim Matane ya ce saboda zuwan damina jami'an tsaron ba lallai ne su iya ssamun damar shiga dazukan ba.

Matane ya ce: "Gwamnatin jiha ta rubuta wa Shugaba Muhammadu wasika da Sufeto Janar na 'yan sanda da Hafsan Sojoji da kuma rundunar sojan sama domin neman agaji.

Kafin haka, mutanen yankin irin su Aisha za su ci gaba zama cikin zulumi da fargabar cira da rayuwarsu daga miyagu a kowacce ranar Allah.

Labarai masu alaka