Yadda majalisar Kano ta tantance kwamishinoni a sa'a 3

Kwamishinonin Kano Hakkin mallakar hoto Facebook/Salihu Tanko Yakasai
Image caption Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinonin jim kadan bayan rantsar da su

A wani mataki na irin karin maganar nan na in ba ka yi ban wuri, majalisar dokokin jihar Kano ta tantance mutum 20 cikin sa'a uku domin nada su a matsayin kwamishinoni.

A ranar Talata ne dai majalisar ta sanya ranar tantance mutanen da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya mika mata domin tantancewa kafin nada su kwamishinoni, kuma 'yan majalisar zartarwar jihar.

Tun gabanin ranar tantancewar dai gwamnatin jihar ta bayyana ranar Talatar da yamma, a matsayin ranar da za a rantsar da kwamishinonin, abin da ke nuna cewa gwamnati tana da tabbacin cewa majalisar za ta tantance mutanen ba tare da wata matsala ba.

A watan Mayun 2019 ma dai majalisar ta Kano ta amince da wani kudurin doka na kirkirar masarautu, inda ta yi karatu na daya da na biyu da na uku kan kudurin dokar a rana daya.

Majalisar dai ta rika cewa da dama daga cikin kwamishinonin cewa "duka ka tafi" bayan wanda ya zo tantancewar ya gabatar da takaitaccen tarihinsa.

Wadanda suka shaida tantancewar da aka watsa kai tsaye a wasu kafofin watsa labarai sun ce, babu wasu tambayoyi na a zo a gani da aka yi wa mutanen da suka je tantancewar.

Hakan dai a cewar wasu, tamkar nuna cewa majalisar ta zama 'yan amshin shatar gwamnati ce.

Sai dai daya daga 'yan majalisar dokokin jihar ta Kano ya ce majalisar ta yi aikinta bisa ka'ida da bin dokokin tantancewa.

Alhaji Salisu Maje Ahmad Gwangwazo, wanda ake fi sani da Alhaji Baba, mai wakiltar mazabar birni da kewaye karkashin jam'iyyar PDP, ya ce majalisar ta yi aiki ne da tantancewar da aka yi wa mafi yawancin kwamishinonin, wadanda suka yi aiki a wa'adin farko na Gwamna Ganduje.

Ya ce, sun takaita tantance mafi yawan mutanen da gwamna ya mika musu ne saboda majalisa ta takwas ta riga ta tantance su, kuma ba a same su da wani laifi da zai bukaci sake tantance su ba.

Alhajin Baba ya kara da cewa, majalisar ta riga ta yi bincike a kan mutanen gabanin zama a zauren majalisar domin tantance su, "don haka abin da jama'a suka gani karashe ne kawai."

To sai dai wasu na ganin baiken majalisar duk da haka, inda ake ganin ya kamata a ce an dauki lokaci wajen tantancewar.

Hakkin mallakar hoto Facebook/Salihu Tanko Yakasai

Labarai masu alaka