Burkina Faso: Mutum 37 sun mutu a hari kan masu hakar ma'adinai

A soldier stand guard outside the headquarters of the country's defence forces in the capital Ouagadougou Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Burkina Faso na fama da hare-haren masu tayar da kayar baya da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane

Akalla mutum 37 ne suka rasa rayukansu, wasu mutum 60 kuma suka sami raunuka a yayin wani hari da aka kai kan wani ayarin motoci dauke da ma'aikatan wani kamfani da ke hako ma'adinai a Burkina Faso.

Rahotannin na cewa an yi wa wasu motocin safa-safa biyar kwanton bauna ne a ranar Laraba kimanin kilomita 40 daga garin Boungou da ke gabashin kasar.

Motocin mallakin wani kamfani kasar Canada ne mai aikin hako ma'adinai a kasar.

An kuma ruwaito cewa an kai wa wata motar sojoji da ke raka ayarin hari da wani abu mai fashe daf da harin da maharan suka kai kan ma'aikata masu hako ma'adinai da ke cikin motocin.

Wannan ne hari irinsa na uku kan ma'aikatan kamfanin Semafo cikin watanni 15 da suka gabata.

Kamfanin ya ce an kai wannan harin ne a kan wata hanya da ke zuwa garin Fada daga wurin da ya ke hako ma'adinai a Boungou.

Kamfanin ya kuma ce harin bai shafi ayyukansa na hako ma'adinai ba, kuma ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan.

"Muna nan muna duba yadda za a inganta tsaro ga dukkan ma'aikatan kamfaninmu, da masu hulda da mu," inji wata sanarwa da kamfanin ya fitar.

Labarai masu alaka