'Tasirin Iran ya wuce na Saudiyya a Gabas Ta Tsakiya'

Members of Iran's Revolutionary Guards Corps (IRGC) at a military parade in the capital Tehran on September 22, 2018 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption dakarun juyin juya hali na kasar Iran IRGC na da fiye da mutum 150,000

Iran tana samun nasara a dabarun da take amfani da su na neman karfin fada a ji fiye da abokiyar hamayyarta Saudiyya a yankin Gabas Ta Tsakiya, kamar yadda wani bincike da wata cibiyar bincike ta kasa da kasa da ke Birtaniya, International Institute for Strategic Studies (IISS) ya nuna.

Abokan hamayyar Iran na yankin sun kashe biliyoyin daloliya wajen sayen makamai daga kasashen yamma, kuma mafi yawa daga Burtaniya suka saya.

Duk da wannan makudan kudi da ake kashewa, Iran wacce aka kakabawa takunkumai ta samu nasarar karuwar tasiri a bangarori masu muhimmanci a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Tana da karfin fada a ji - wanda ya samo asali ta hanyar samun damar iko a wasu lamuran da suka hada da abin da ya shafi Syria da Lebanon da Iraki da kuma Yemen.

'Cusa ra'ayi'

Sai dai kafa kungiyoyin da Iran take yi na 'yan tawaye a fadin Gabas Ta Tsakiya, wadanda suke taya ta yaki da gwamnatocin yankin ba sabon abu ba ne.

Tun bayan da kasar ta fara kafa Kungiyar Hezbollah a Lebanon, sai take ta neman yadda za ta dinga cusa ra'ayinta na juyin juya hali ga wasu kasashen da kuma fadada tasirinta a sauran wurare tun bayan komawar Ayatollah Ruhollah Khomeini Tehran a shekarar 1979.

Amma rahoton Cibiyar IISS mai shafi 217, mai taken "Iran's Networks of Influence in the Middle East", (Tasirin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya), ya samar da bayanan da ba su taba bayyana ba kan ayyukan da Iran ke yi a yankin.

Rahoton ya ce, "Jamhuriyyar Musulunci ta Iran ta karkato da hankulan kasashen duniya kanta a matsayin kasa mai karfin fada a ji a yankin Gabas Ta Tsakiya."

Mawallafan sun kuma ce: "Ta samu wannan nasara ce ta hanyar kalubalantar manyan kasashe da tasiri kan wasu aikace-aikacenta da kuma amfani da wasu dabaru na bayan gida."

Abu mafi muhimmanci a nan shi ne amfani da wata runduna ta dakarun juyin juya hali na kasar Iran da ke aiki a kasashen waje IRGC.

Da dakarun juyin juya halin da shugabansu Manjo Janar Qasem Soleimani suna aiki ne karkashin umarnin jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamanei, wanda hakan ya sa suka kauce wa tsarin gudanarwa na rundunar sojin kasar da hakan ya sa suka zama wani bangare mai cin gashin kansa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manjo Janar Qasem Soleimani ne jagoran dakarun juyin juya hali na kasar Iran

Tun bayan da Amurka ta jagoranci hambare gwamnatin Saddam Hussein a 2003, dakarun juyin juya hali sun kara kaimi a Gabas Ta Tsakiya inda suke bayar da horo da taimakon kudi da kuma makamai ga mayaka wadanda ke tare da Tehran.

Kuniyar kuma ta kware wajen yakin sunkuru kamar na ruwa da na jirgi marar matuki da kuma intanet. Hakan na bai wa Iran damar kuntatawa makiyanta masu muggan makamai yaki.

A watan Afrilu, Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana dakarun IRGC tare da dakarun juyin juya hali a matsayin kungiyoyin 'yan tadda (FTO). Wannan shi ne karon farko da Amurka ta kira dakarun wata gwamnati a matsayin 'yar ta'adda.

Iran ta mayar da martani inda ita ta ayyana dakarun Amurka da ke a yankin kasashen Larabawa a matsain 'yan ta'adda. Wannan kawai dai a baki ne.

Jak Sraw, wanda shi ne sakataren harkokin kasashen waje na Birtaniya tsakanin shekarar 2001 zuwa 2006, wanda ya ziyarci Iran sau da dama, na ganin cewa rawar da Janar Soleiman ke takawa ta fi karfin ta kwamanda kawai.

"Qasem Soleimani ne ke kula da harkokin kasashen waje a yankin ta hanyar amfani da abokan kawancensu da karfi," a cewarsa.

A jawabinsu kan rahoton IISS, mai magana da jawon ofishin jakadancin Iran a Birtaniya ya shaida wa BBC cewa: "Idan rahoton na nufin a daraja ikon da Iran take da shi a yankin, to wannan abin maraba ne.

"Tsarin yin ko in kula da Iran bai yi aiki ba. Iran ta ki. Iran ta yi nasarar iyakance ta'addancin tattalin arziki. Eh, ita kasa ce mai karfi kuma tana da abokan kawance masu yawa da shirin kawance a yankin."

Hezbollah - 'Kananan abokan kawance'

Kungiyar Shi'a ta Hezbollah wadda ita jam'iyyar siyasa ce kuma ta mayaka "ta samu wani matsayi na musamman cikin kawayen Iran a cewar rahoton wanda ya yi bayanin yadda ake kai abubuwa Syria da Iraki.

Hezbollah ta taka rawa ta musamman a rikicin da ke faruwa a kasashen biyu inda suke yakin tare da sojojin da suke biyayya ga Shugaba Bashar al-Assad da kuma taimakon mayaka 'yan Shia.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wadannan magoya bayan Hezbolla a Beirut na dauke da hoton shugaban Iran Ayatollah Ali Khamenie

Amma rahoton ya ce Hezbollah "kamar wata kanwa ce da abokiyar gwagwarmaya ga Iran" amma kungiyar ta zama wata jigon kungiyoyin gwagwarmaya ga Larabawa da jam'iyyun siyasa da kuma Iran.

Shiga cikin Iraki da Syria

Mamaye Iraki da hambare gwamnatin Saddam Hussein ya sauya yanayin Gabas Ta Tsakiya da kuma ba wai Iran damar yin amfani da wannan damar.

Kafin wannan lokacin kasashen Larabawa na ganin cewa mulkin Iraki da 'yan sunni suka yi a matsayin wata garkuwa a kan yaduwar Iran.

Yanzu da wannan katangar ta tafi, Iran ta yi amfani da kusancinta na al'ada da addini ta shiga Iraki, wadda ke da rinjayen Larabawa 'yan Shia inda ta zama mafi karfi a kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar gangamin gaggagwa (PMU) sun yi yaki tare da dakarun Iraki kan 'yan kungiyar IS

Ta bayar da makamai kuma ta bayar da horo ga dakarun da ake kira Popular Mobilisation Unit (PMU) wadanda suka taimaka wajen cin galabar IS amma 'yan Iraki na ganin hakan a matsayin mulkin mallaka.

Amma Iran ba duka ta samu yadda take so ba. Zanga-zanga da rikici da ke aukuwa a Iraki na nuna cewa matasa ba su jin dadin gwamnatinsu wadda Iran ke mara wa baya.

Rahoton ya ce "PMU ta sauya daga masu kishin kasa zuwa ga masu iko a kasar wanda hakan ya sa sun rasa goyon baya."

Labarai masu alaka