'Tun da aka sace ni a hanyar Kaduna na daina tafiya da mota'

Manir Awal Addo
Image caption Manir Awal Addo ya daina bin hanyar a mota bayan da aka yi garkuwa da shi

Domin gujewa satar mutane don kudin fansa, dubban matafiya ne suka kauracewa bin motoci suke bin jirgin kasa a kullum a hanyar Abuja da Kaduna.

Mannir Awal Addo, wani dan kasuwa ne da ke Abuja amma iyalinsa na Kaduna, an sace shi a babbar hanyar Abuja-Kaduna a farkon shekarar nan, kuma ya zauna wajen masu satar mutanen tsawon kwana biyar.

Ya shaida wa BBC cewa sai da ya biya naira 500,000, kwatankwacin dala 1,300 kafin su sake shi: "Al'amari ne mai cike da tashin hankali."

Ya ce ya yi fama da cutar shan inna da yana yaro don haka bai iya gudu don tsira ba lokacin da masu garkuwar suka tsayar da motar da yake bulaguro a ciki.

"Gaskiya tun daga lokacin na daina tafiya a mota saboda ina matukar tsoron hanya. Hankalina ya fi kwanciya idan na bi jirgin kasa saboda tsaro."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sanda na yi wa jirgin rakiya

Tafiya tsakanin biranen biyu da mota ta fi sauki kuma ta fi araha, kilomita 150 ne, amma kuma lamarin ya dawo na rayuwa da mutuwa ta yadda ake sace gomman mutane a kan babban titin, wasu kuma ake kashe su.

Sai dai a iya cewa godiya ga bashin dala miliyan 500 da China ta bayar aka gina titin dogo daga Abuja zuwa Kaduna wanda ya fara aiki a shekarar 2016 kuma mutane sun fi amfani da shi saboda zamanancin sa, ganin cewa dukkan layukan dogon kasar tsoffi ne tun na zamanin Turwan mulkin mallaka.

Ruguntsumin sayen tikiti

Abu ne mawuyaci samun tikitin yin tafiya a cikin jirgin da yake zirga-zirga sau hudu a rana, inda kusan mutum 5,000 ne ke neman sayensa.

Bukatar tana da girma sosai musamman saboda akwai 'yan sanda guda tara masu dauke da bindigogi domin bayar da tsaro.

Farashin tikitin yana kamawa ne daga naira 1,300 zuwa 1,500 karamar kujera, sai kuma babbar kujera kan naira 3,000 - akan samu dogon layi kafin sayen kowanne daya daga ciki.

Mutane da dama kan rasa tikiti saboda dogon layi. Ma'aikatan da ke aiki a Abuja da damansu suna zaune ne a Kaduna.

A watan Agustan da ya gabata an wallafa wasu hotuna a shafukan sada zumunta na fasinjoji suna ruguntsumi wurin sayen tikiti.

Sai dai an sha zargin jami'ai da ma'aikata a tashar jirgin da yin zamba wurin sayar da sayar da shi, inda suke boyewa sannan su sayar da shi a farashi mai tsada.

Wannnan ta sa gwamnati ta ce tana tunanin za ta mayar da sayen tikitin ta hanyar intanet.

Kazalika, wadanda ba su samu samu tikitin kujera ba za su iya sayen na tsayuwa, sai dai babu bambanci a farashi.

Yayin da na hau jirgin na tarar da sama da mutum 50 suna taye a taragon da nake. Wasu suna maleji tsakanin hanyar tsakiyar jirgin da kuma kofar ban daki.

Image caption Mutane sun gwammace su yi tafiyar a tsaye kan su bi titi

Mutane da dama sun gwammace su yi tafiyar a tsaye sama da su bi hanyar da ake yi wa lakabi da wadda ta fi kowacce hadari a Najeriya.

Gefen hanyar Abuja zuwa Kaduna cike take da bishiyoyin darbejiya da kuka, abin da ke bai wa masu garkiuwa da mutane damar cin karensu babu babbaka.

Masu garkuwar kan dauki talaka da mai kudi ba tare da wani bambanci ba, kuma sukan nemi kudin fansa da ya kai kusan miliyan 50.

A wasu lokuta sukan kashe wadanda suka gaza biyan abin da suka nema.

Image caption Fasinjoji sun fi aminta da jirgin

"Wani lokacin akan samu rahoton garkuwa da mutane sau 10 a rana daya kuma gungu na masu garkuwar kusan 20 ne ke aikace-aikacensu a hanyar.

Babu mamaki kididdigar ta wuce haka domin kuwa iyalai kamar na Addo ba su yarda su kai wa 'yan sanda rahoto ba. Sun zabi su tattauna da 'yan garkuwar kai-tsaye.

Wani dalibi mai karatun digiri na biyu Idris Mohammed, wanda ke bin hanyar duk karshen mako, ya ce ya gwammace ya biya ninkin kudin tikitin "saboda yanzu hanyar ta zama mai hadarin gaske".

Me yasa mutane ba za su zauna a Abuja ba?

Ga mafi yawan ma'aikatan da ke zaune a Abuja ba za su iya biyan naira miliyan daya zuwa miliyan biyar ba (na mai karamin karfi) a matsayin kudin haya duk shekara.

Tun daga sanda ta zama babban birnin Najeriya a shekarar 1991, Abuja ta zama matattarar ma'aikatan diflomasiyya da kuma kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje.

An zabe ta ne kuma saboda kasancewarta a tsakiyar kasar. Mutane da yawa suna shiga birnin domin yin aiki, a saboda haka ne yake kasancewa fayau a karshen mako.

Su kuwa masu garkuwa na amfani ne da wannan dama domin tarewa tare da sace matafiyan.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Yanzu sai 'yan tsiraru masu kwarin rai ne ke iya bin hanyar Abuja-Kaduna

Wadanda ke bin hanyar yanzu sun mika lamuransu ne ga wuraren duba ababen hawa na jami'an tsaro da ake samu nan da can yayin tafiyar.

Duk da cewa 'yan sanda sun samu 'yar nasara a kan miyagun, ciki har da kame wani kasurgumin dan fashi a jihar Legas a shekarar 2017, har yanzu wasu na nuna shakku game da yunkurin nasu na kawo karshen masu garkuwar.

Image caption Tashar Rigasa da ke Kaduna ce zangon jirgin na karshe

Zuwa yanzu dai samuwar jirgin abin farin ciki ne babba kuma matsalar tsaron da aka samu ta baya-bayan nan dabbobi kawai ta shafa.

A watan Satumban bara 'yan sanda sun yi harbi a sama domin raraka mazauna wani kauye da suka taru domin kai hari ga jirgin kasan, bayan jirgin ya take shanu kusan 50 yayin da suke tsallaka titinsa.

Tashar jirgin ta zama wata mahadar talaka da mai kudi kuma takan hada wadanda ke fada da juna a wasu yankuna, sai dai dukansu suna neman tsira ne daga miyagu.

Lokacin da muka isa tashar Rigasa ta Kaduna mutane sun daga hannayensu sama suna addu'a saboda sun isa ba tare da an sace su ba.

Labarai masu alaka