'Makashin maza' zai yi zaman kaso na shekara 30

Bosco Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kotun hukunta manyan laifukan ta duniya, ICC, ta yanke wa tsohon madugun 'yan tawayen kasar Congo, Bosco Ntaganda hukuncin zaman gidan kaso na shekara 30, bisa laifukan yaki da cin zarafin mutane.

An dai tuhumi Bosco Ntaganda wanda ake yi wa lakabi "Terminator" ko 'makashin maza' da laifuka 18 da suka hada da kisan jama'a da fyade da lalata mata da amfani da kananan yara a aikin soja.

Alkalan kotun ta ICC sun gano cewa a watan Yuli mayaka masu goyon bayan Ntaganda sun aikata kisan kare dangi.

Wannan ne dai karon farko da kotun ta ICC ta yanke hukunci mafi tsayi ga wani.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wane ne Bosco Ntaganda?

  • An haife shi 1973 a Rwanda, inda ya girma
  • Ya tsere zuwa DR Congo lokacin da yana matashi bayan da aka kai wa 'yan Tutsis hari
  • A shekara 17, ya fara shiga kungiyar mayakan sa-kai a Rwanda da DR Congo
  • 2002-3: Ya zama mayaki a yankin Ituri na kasar congo
  • 2006: Kotun ICC ta same shi da laifin daukar yara shiga yaki a Ituri
  • 2008 Ya zama jagoran dakarun da suka gudanar da kisan kiyashi kan mutum 150 a Kiwanji
  • 2009: Ya shiga aikin sojan kasar Congo inda ya zama janaral
  • 2012: Ya fice daga aikin soja inda ya janyo tawayen da ya haddasa mutum 800,000 suka bar matsugunansu
  • 2013: Ya mika kai ga ofishin jakadancin Amurka a Kigali, Rwanda, bayan da kan 'yan tawayen da ayke jagoranta ya rabu
  • 2019: Kotun ICC ta same shi da laifukan yaki inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na shekara 30