Masu bore sun yi wa shugabar karamar hukuma aski a Bolivia

Patricia Arce Hakkin mallakar hoto EPA

Shugabar karamar hukumar a kasar Bolivia ta fuskanci boren masu zanga-zanga inda suka tilasta mata tafiya a kasa ba takalmi sannan suka yi mata aski da shafe mata kai da fenti.

An dai kai Patricia Arce ta jam'iyya mai mulki wurin 'yan sanda bayan wasu 'yan awoyi.

Wannan ne dai artabu na baya-bayan nan tsakanin magoya bayan gwamnati da na hamayya tun bayan gudanar da babban zaben kasar.

Akalla mutum uku ne suka mutu kawo yanzu.

Wata kungiyar masu zanga-zangar kin jinin gwamnati sun toshe wata gada a garin Vinta wanda gari ne a lardin Cochabamba a tsakiyar Bolivia, a ci gaba da nuna turjiya ga sakamakon zaben kasar na ranar 20 ga watan Oktoba.

Masu zanga-zangar dai na zargin shugabar karamar hukumar da hannu wajen hukuncin da jami'an tsaro ke yi musu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto EPA