Ibrahimovic zai koma AC Milan

Zlatan Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto Reuters

Zlatan Ibrahimovic ya shirya tsaf domin komawa AC Milan lokacin da kwantaraginsa ta kare a LA Galaxy, in ji Don Garber.

Dan wasan dan kasar Sweden dai ya je LA Galaxy a watan Maris 2018 inda kuma kwantaraginsa yake karewa a karshen wannan shekara.

Ibrahimovic ya taka leda a kulob din Milan a tsakanin 2010 zuwa 2012, inda ya ci musu kwallaye 42 a wasannin 61.

Wasan da ya buga a baya-bayan nan shi ne lokacin da LA Galaxy ta ci Los Angeles FC 5-3.

Ibrahimovic ya zura kwallaye 53 a lokacin yana Amurka inda aka ayyana sunansa a jerin fitattun 'yan wasa a 2018 zuwa 2019.