An tsinci hannayen wata mace a jakar wani farfesa a Rasha

Prof Sokolov sanye da kayan tarihi na sojojin Rasha Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Prof Sokolov sanye da kayan tarihi na sojojin Rasha lokacin wani biki

Lauyoyi a Rasha sun ce wani sanannen farfesa masanin tarihi a kasar ya tabbatar da zargin da ake masa na kashe masoyiyarsa - kuma tsohuwar dalibarsa, bayan da aka kama shi a wani rafi dauke da wata jaka da ta kunshi hannuwan marigayiyar.

Kafafen yada labarai sun ce an kama farfesan ne mai suna Oleg Sokolov, mai shekara 63 a cikin rafi dauke da jakkar mai kunshe da wasu sassa na jikin tsohuwar budurwar tasa, inda ya je domin jefarwa.

Daga nan ne sai 'yan sanda suka gano ragowar gangar jikin marigayiyar mai suna Anastasia Yeshchenko, a gidansa.

Farfesa Sokolov mutum ne da ya shahara, har ma ya samu lambar yabo ta L├ęgion d'Honneur ta kasar Faransa.

"Ya amsa laifinsa," in ji lauyansa mai suna Alexander Pochuyev. Ya kuma ce farfesan ya yi nadamar abin da ya aikata, inda yanzu yake bai wa masu bincike hadin kai.

Rahotanni sun ce farfesan ya shaida wa 'yan sanda cewa shi ne ya kashe matar bayan wani sabani da ya shiga tsakanin su, inda ya fille mata kai da hannuwa, da kuma kafafunta.

An ce ya shirya cewa shi ma zai kashe kansa ne bayan ya batar da gawar tata baki daya.

Lauyansa ya ce yana iya yiwuwa farfesan na fama ne da damuwa, kasancewar yana karbar maganin cutar sanyin jiki daga asibiti.

Farfesan masanin tarihi ya rubuta litattafai da dama, inda shi da tsohuwar budurwar tasa suka hada hannu wajen rubuta wasu daga cikinsu.

Shi da marigayiyar masana ne na tarihin kasar Faransa, inda sau da dama sukan sa dadaddun kaya irin na tarihi.

Dalibansa sun bayyana shi a matsayin mai hazaka.

Labarai masu alaka