Hotunan Afirka na wannan makon: 1-7 Nuwamban 2019

Ga wasu zababbun hotuna na wasu abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan.:

Dan wasan Rugby na Ingila Anthony Watson (C) lokacin da ya gamu da naAfirka ta kudu a wasan karshe na cin kofin wasan Rugby a Japan ranar 2 ga watan Nuwamba, 2019. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Asabar kungiyar Rugby ta Afirka ta kudu a wasan da suka buga da Ingila
'Yan wasan Rugby na Afirka ta kudu bayan da suka lashe kofin duniya na gasar kwallon zari-ruga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'yan wasan Rugby na Afirka ta kudu
Prince Harry, ya na taya Faf de Klerk na Afirka ta kudu murna bayan da kasarsa ta lashe kofin duniya na kwallon Rugby. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Faf de Kerk tare da yarima Harry bayan lashe kofin duniya na kwallon Rugby
Yadda mutane sanye da kananan kaya suka tarbi 'yan wasan kwallon Rugby wadanda suka lashe kofin duniya a kan titunan Johannesburg ranar 7 ga watan Nuwamba, 2019 in Johannesburg, South Africa. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda mutane sanye da kananan kaya suka tarbi 'yan wasan kwallon Rugby wadanda suka lashe kofin duniya
Mahaya babura sun nishadantar da al'umma a Ougadougou na kasar Burkina Faso a ranar Lahadi, rana ta karshe ta gasar tseren babura na Tour du Faso. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mahaya babura sun nishadantar da al'umma a Ougadougou na kasar Burkina Faso a ranar Lahadi, rana ta karshe ta gasar tseren babura na Tour du Faso.
Yadda wani mai hada alawa ya dauki hoton abubuwan da ake hadawa na shirye-shiryen bukukuwan Maulidin annabi Muhammad SAW da za a yi ranar Litinin a birnin Alkahira na kasar Masar. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda wani mai hada alawa ya dauki hoton abubuwan da ake hadawa na shirye-shiryen bukukuwan Maulidin annabi Muhammad SAW da za a yi ranar Litinin a birnin Alkahira na kasar Masar.
Ambaliyar ruwa ta daidaita wasu sassa na kasar Sudan ta kudu a ranar Laraba. Yadda wata yarinya ke ratsawa ta cikin ruwa da ya yi ambaliya. 6 ga watan Nuwamba, 2019. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ambaliyar ruwa ta daidaita wasu sassa na kasar Sudan ta kudu a ranar Laraba. Yadda wata yarinya ke ratsawa ta cikin ruwa da ya yi ambaliya.
Zakaran wasan gudun yada-kanin-wani na birnin New York, Geoffrey Kamworordaga daga kasar Kenya, a ranar Lahadi 3 ga watan Nuwamba, 2019. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zakaran wasan gudun yada-kanin-wani na birnin New York, Geoffrey Kamworordaga daga kasar Kenya, a ranar Lahadi
...Girma Bekele Gebre na kasar Ethiopia ne ya zo na uku, inda ya kare da kyar a gudun yada-kanin-wani na birnin New York City Marathon a 3 ga Watan Nuwamba, 2019. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption ...Girma Bekele Gebre na kasar Ethiopia ne ya zo na uku, inda ya kare da kyar.
A ranar Juma'a, mutane a Algeria sun fito domin neman sauyin gwamnati a birnin Algiers ranar 1 ga watan Nuwamba, 2019. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Juma'a, mutane a Algeria sun fito domin neman sauyin gwamnati.
...daya daga cikin masu zanga-zanga na kasar Algeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption ...daya daga cikin masu zanga-zanga na kasar Algeria
A birnin Canakry na kasar Guinea, an kona tayoyi a lokacin jana'izar wani da aka kashe lokacin zanga-zangar kin amincewa da sake takarar shugaba Alpha Conde a karo na uku. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A birnin Canakry na kasar Guinea, an kona tayoyi a lokacin jana'izar wani da aka kashe lokacin zanga-zangar kin amincewa da sake takarar shugaba Alpha Conde a karo na uku.
Wani yaro na kallo sa'ilin da firaminista ya kai ziyara a sansanin yan gudun hijira na Darfur da ke Sudan. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani yaro na kallo sa'ilin da firaminista ya kai ziyara a sansanin yan gudun hijira na Darfur da ke Sudan.
Daga bangare guda kuma a sansanin 'yan gudun hijrar na El-Fasher, wasu mata na kan hanyarsu zuwa aiki. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daga bangare guda kuma a sansanin 'yan gudun hijrar na El-Fasher, wasu mata na kan hanyarsu zuwa aiki.
Yadda rana ta fada a rairayin Sahara na kasar Moroco, a ranar Juma'a. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda rana ta fada a rairayin Sahara na kasar Moroco, a ranar Juma'a.

Hotuna daga AFP, Getty Images, Nur Photo, da Anadolu Agency

Labarai masu alaka