Equatorial Guinea ta nada Migne a matsayin koci

Sebastien Migne Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar kwallon kafar kasar Equitorial Guinea na fatan dan kasar Faransa, Sebastien Migne zai yi wa kungiyar wasan kasar jagora ga gaci.

Migne zai maye gurbin Angel Lopez dan kasar Sipaniya kafin bikin bude wasannin neman gurbin shiga gasar zakarun nahiyar Afirka ta 2021.

Maigne mai shekara 46 ya rattaba hannu kan kwantaragin da a koyaushe za a iya dakatar da ita bayan watanni shida.

Wasan da zai fara jagoranta shi ne wanda kasar za ta buga da Tanzania a ranar 15 ga watan Nuwamba sai kuma wasan da Equitorial Guinea za ta da Tunisia.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba