Kamaye da Adama
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

"Dadin Kowa": 'Abin da ya sa nake fitowa a talaka futuk'

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Fitattun taurarin da ke fitowa a shahararren wasan kwaikwayon nan na arewacin Najeriya wanda ake nunawa a talbijin, "Dadin Kowa", Adama da Kamaye, sun ce ba karamin farin jini wasan ke jawo masu ba a wajen mutane.

Dan Azumi Baba, wanda ake kira Kamaye a shirin, ya kuma ce yana fitowa a matsayin talaka futuk ne a fim din saboda haka darakta ya bukaci ya yi, kuma hakan ya sa a zahiri mutane suna nuna mishi so da tausayi.

Ita kuma Hajiya Zahra'u Sale, wadda ke fitowa a matsayin Adama matarsa, ta ce rawar da take takawa a fim din ta masifaffiya mara tausayin miji, ta sa wasu ke tunanin haka take a zahiri, yayin da wasu kuma ba sa nuna mata wata kyama.

A hirarsu da BBC sun kuma fadi yadda suka fara fim da burinsu a nan gaba.

Ku kalli bidiyon da ke sama domin ji daga bakin taurarin biyu.

Bidiyo: Fatima Othman

Labarai masu alaka