Brazilian ex-President Lula freed from jail
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli bidiyon lokacin da aka sako tsohon shugaban Brazil daga kurkuku

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon yadda aka sako Mista Silva

Tsohon shugaban Brazil Luiz InĂ¡cio Lula da Silva ya taras da dubban magoya bayansa suna jiransa a gaban gidan kurkukun da aka tsare shi a birnin Curitiba.

Wani alakalin kotun kolin kasar ne ya bayar da umarnin a sako shi, bayan da kotun ta yanke hukunci cewa ba za a iya tsare mutum a gidan yari ba idan yana da sauran damar daukaka kara.

Tsohon shugaban ya lashi takobin wanke kansa daga dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, kuma ya soki abin da ya kira "rubabben bangaren shari'a", da ya ce ya hada baki da "'yan siyasa".

Labarai masu alaka