Wadanne manyan labarai ne suka faru a Najeriya a makon jiya?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

BBC ta tsakuro maku muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya daga ranar 3 zuwa 8 ga watan Nuwamba, 2019.

Martanin fadar shugaban kasa kan rage yawan ma'aikatan Osinbajo

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce dole ce ta sa a soke wasu mukamai karkashin ofishin mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo, da nufin rage yawan kashe-kashen kudaden kasa.

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu ya ce "Fadar shugaban kasa na son yi wa tsarin mukaman gwamnati kwaskwarimar da ba a taba gani ba, wanda zai shafi mukaman siyasa da dama da ko dai aka soke su ko kuma ba a sabunta su ba a zango na biyu na mulki."

Ya kuma ce shugaban kasa ne ya bayar da umarnin yin hakan a wani mataki na rage kashe kudaden gwamnati, kasancewar mukamai sun yi yawa a fadar shugaban kasa, al'amarin da ke janyo kashe kudade fiye da kima.

Boko Haram ta mamayi sojojin Najeriya har ta 'kashe' 10

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wata majiyar sojin Najeriya ta ce sojoji 10 sun mutu sakamakon wani harin kwantan bauna da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai kan sojojin Najeriya a garin Domboa na jihar Borno, ranar Laraba.

Har wa yau, sojoji 12 sun yi batan dabo bayan harin na ranar Laraba, kamar yadda wata majiyar soji da ba ta son a ambaci sunanta ta shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP, ranar Alhamis.

"Mun rasa sojoji 10 a lokacin wani artabu da 'yan ta'adda da suka yi wa sojojinmu kwantan bauna yayin wani sintiri a yankin." In ji majiyar ta soja.

An sa dokar hana sayar da mai a yankunan kusa da iyaka

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya ta bayar da sanarwar dakatar da safarar man fetur zuwa gidajen man da ke kusa da kan iyakokin kasar da zuwa nisan kilomita 20.

Hukumar ta ce ta dade tana zargi kan yawan gidajen man fetur din da ake budewa a yankunan da ke daf da kan iyakoki, wadanda ga alama ana amfani da su ne wajen fasa-kwauri. Sai dai lamarin bai yi wa wasu mazauna yankunan dadi ba.

Najeriya ta tafka asarar dala biliyan 42 cikin shekara 10

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani rahoto da hukumar hukumar tabbatar da gaskiya a harkar hakar ma'adinai ta Najeriya (NEITI) ta fitar ya nuna cewa kasar ta yi hasarar kudi dala biliyan 42 sanadiyyar ayyukan masu satar danyen da kuma tataccen man fetur a kasar cikin shekara 10.

A cewar hukumar kudin da kasar ta yi asara ta wannan hanya cikin shekara guda da wasu watanni sun isa a cike gibin da ke cikin kasafin kudin kasar na shekarar 2020.

An zargi Buhari da mayar da Osinbajo saniyar-ware

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar kabilar Yarbawa ta Afinifere ta zargi shugaba Muhammadu Buhari da kokarin mayar da mataimakinsa Yemi Osinbajo gefe a ayyukan gwamnati, bayan da ya ki mika masa rikon shugabancin kasar a lokacin da zai yi tafiya zuwa Birtaniya.

Wannan zargi ya taso ne bayan da aka kai wa shugaba Buhari dokar hako mai na cikin teku da kan tudu har London domin sanya mata hannu bayan amincewar majalisar dokokin kasar.

An ruwaito mai magana da yawun kungiyar ta Afinifere Yinka Odumakin na cewa nuna wariya ga Yemi Osinbajo wani abu ne da aka tsara.

Sai dai daga baya fadar gwamnatin kasar ta musanta cewa akwai rashin jituwa tsakanin shugaban kasar da mataimakinsa.

Jihar Kano ta haramta ayyukan gidan-mari

Gwamnatin Kano ta bayar da umurnin rufe gidajen mari da ake da su a fadin jihar har zuwa lokacin da gwamnati ta fitar da tsarin da ya dace na tafiyar da irin wadanna cibiyoyi.

Shugaban kwamitin kula da makarantun tsangayu a jihar Dr Muhammad Tahir Adamu ne ya sanar da daukar matakin, kuma sanarwar da ya fitar ta ce matakin bai shafi makarantun islamiya da na allo ba.

Pantami ya ba hukumar sadarwa wa'adin rage kudin data

Hakkin mallakar hoto TWITTER

Ministan sadarwa da harkokin intanet na Najeriya ya bai wa hukumar sadarwa ta Najeriya izinin ta lalubo hanyoyi da za a rage tsadar farashin data a kasar cikin kwana 5.

Ya bayar da wannan umurni ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gudanarwar hukumar ta NCC, karkashin jagorancin Senator Olabiyi Durojaiye.

Pantami ya ce yana karbar koke-koke da dama daga al'umma game da tsadar kudin sayen data na shiga intanet a kasar.

Nigeria ta ba da sharudda kafin ta bude iyakokinta

Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI

Gwamnatin Najeriya ta bai wa kasashen da ke kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta yamma, ECOWAS, wasu sharudda, wadanda ta ce dole su cika su, kafin ta bude bakin iyakokinta.

Ministan harkokin wajen kasar, Geoffrey Onyeama, ya bayyana sharuddan wadanda suka shafi zirga zirgar mutane da kayayyaki ta bakin iyaka, a wajen wani taron kwamitin da ke sa ido kan rufe wasu iyakokin kasar da aka yi a Abuja. Sharuddan su ne:

  • Najeriya ba za ta yarda a rinka shigo da kayan da aka sauya wa mazubi a makwabtan kasashe ba.
  • Dole a rushe dukkanin wuraren ajiye kayayyakin da ke bakin iyaka ko kusa da iyakokin Najeriya.
  • Dole ne a yi wa kayayyakin da za a shigo da su daga makwaftan kasashe rakiya.
  • Mutanen da ke da fasfo ne kawai za a bari su ketaro cikin kasar.

Buhari ya taka wa kamfanonin mai burki kan rijiyoyin mai

Hakkin mallakar hoto TWITTER

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin yi wa dokar rijiyoyin cikin teku da tsarin kwangilar samar da mai ta doron kasa gyaran fuska wadda ta fayyace yadda za a kasa ribar mai da ake sayarwa fiye da dala 20 a kasuwar duniya.

Ya sa hannu kan dokar ne kimanin mako biyu bayan majalisar dokokin kasar ta amince da kudirin inda ta mika ga fadar shugaban kasa.

Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter da yammacin ranar Litinin cewa ya rattaba hannu kan kudirin dokar: