Hotuna: Yadda aka gudanar da bukukuwan mauludi a duniya

Musulmi a kasashen duniya daban-daban sun gudanar da bukukuwan maulud, inda da dama suka yi tattaki da tarukan yabo ga annabi Muhammad SAW.

Bayanan hoto,

Mai fafutuka a kasar Indiya, Swami Agnivesh yana daga wa jama'a hannu a lokacin tattakin bikin tuna wa da haihuwar annabi Muhammadu SAW a Mumbai.

Bayanan hoto,

Yara sun yi wa mota ado da balan-balan lokacin tattakin murnar Mauludi a Mumbai, Indiya.

Bayanan hoto,

Dandazon masu kwanan zaune domin sauraron karatu na murnar mauludin annabi Muhammad SAW, a Dakar na Senegal.

Bayanan hoto,

Wani bangare na masu mauludi a birnin Dakar na kasar Senegal.

Bayanan hoto,

Yadda masu bikin mauludi suka kawata birnin Kairouan na kasar Tunisia yayin bukuwan maulud.

Bayanan hoto,

Wasu musulmi a bakin wani masallaci a garin Yogyakarta na Indonesia yayin bikin maulud.

Bayanan hoto,

Yadda wasu musulmi suka yi ta raye-raye da kade-kade a bikin maulud din a birnin Tripoli na kasar Lebanon.

Bayanan hoto,

Masu bikin mauludi a kasar Indonesia, inda suka dauki wani shuci mai kama karaga domin alamta wani muhimmin abu dangane da ranar Mauludi.

Bayanan hoto,

Wani mutum da dansa kan doki domin bikin maulud a birnin New Delhi na Indiya.

Bayanan hoto,

Tsaffi ke nan ke addu'o'i na musamman a lokacin bukukuwan maulud a yankin Kashmir.

Bayanan hoto,

Masu bikin maulud sun yi dandazo a dandalin al-Sabin Square a birnin Sana'a na kasar Yemen.

Bayanan hoto,

Daruruwan musulman da suka yi tattaki domin tuna wa da ranar haihuwar annabi Muhammad SAW a birnin Kuala Lumpur na Malaysia.

Bayanan hoto,

Wasu masu tattakin murnar maulud rike da tutokci a birnin Kumasi na Ashanti da ke kasar Ghana.

Bayanan hoto,

Wani bangaren mata masu murnar maulud a birnin Kumasi na Ghana.

Bayanan hoto,

Mataimakin shugaban kasar Ghana, Alhaji Mahmudu Bawumia ke gaisa wa da wani malami a wurin bikin maulud a birnin Kumasi na Ghana.

Bayanan hoto,

Babban limamin kasar Ghana, Sheikh Dr Usman Nuhu Sharubutu yake addu'o'i a lokacin bikin mauldu a birnin Kumasi.

Bayanan hoto,

Wani bangaren masu tattakin murnar mauludi a birnin Abuja.

Bayanan hoto,

Bangaren masu zikiri da rera yabon annabi domin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Bayanan hoto,

Sahun 'yan mata 'yan makaranta a lokacin tattakin bikin mauludi a birnin Abuja.

Bayanan hoto,

Wani bangaren masu zikiri da yabon annabi lokacin jerin gwanon mauludi ranar Litinin a birnin Abuja.