Yadda jinin aladu ya gurbata ruwan kogi a Koriya Ta Kudu

The river having turned red after the pigs were killed Hakkin mallakar hoto Yeoncheon Imjin River Civic Network
Image caption Ruwan da aka yi mai karfi ya kora jinin aladun daga inda aka yanka su zuwa Kogin Imjin

Ruwan wani kogi a kan iyakar Koriya ya gurbace da jinin aladu.

Hukumomi a Koriya Ta Kudu sun kashe aladu 47,000 a wani kokari na hana yaduwar cutar murar aladun Afirka.

Ruwan da aka yi mai karfi ya kora jinin aladun daga inda aka yanka su zuwa Kogin Imjin.

Cutar murar aladun Afirka dai tana da muni kuma ba ta warkewa, kuma da wuya duk aladen da ya kamu da ita ya rayu, amma cutar ba ta yi wa mutane illa.

Hukumomi a yankin sun yi watsi da damuwar da aka nuna cewa jini na iya janyo yaduwar cutar murar aladun ga wasu dabbobin da ke fusknatra barazanar kamuwa da ita, inda suka ce an dauki mataki kafin a yanka aladun.

Sun kuma ce an dauki matakan gaggawa don kare lalacewar muhalli.

Yaduwar cutar a Asiya

An fara aikin yanka aladun ne a karshen makon da ya gabata. An kwashi aladun ne a cikin manyan motoci inda aka kai su kan iyaka kusa da makabarta.

Rashin kai robobin da za a kwashe su a ciki bayan an yanka ya jawo tsaikon da ba a kammala aikin da wuri ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An bai wa sojojin Koriya Ta Arewa umarnin kashe duk wani aladen daji da aka ga yana tsallake iyakar kasar

A kwana-kwanan ne aka gano cutar murar aladu a Koriya Ta Kudu, kuma ba a samu jita-jitar cewa aladu ne suka yada ta ba, wadanda ke ketare iyakokin Koriya Ta Arewa ko Kudu da ke da tsaro ba.

A watan Mayu ne aka fara samun cutar murar aladu a Koriya Ta Arewa, kuma Koriya Ta Kudu ta yi matukar kokari don ganin abin bai yadu zuwa kasarta ba.

An bai wa sojojin Koriya Ta Arewa umarnin kashe duk wani aladen daji da aka ga yana tsallake iyakar kasar.

Duk da wadannan matakai da take dauka, sai da Koriya Ta Kudu ta samu bullar cutar a karon farko ranar 17 ga watan Satumba.

Yawancin kasashen yankin Asiya sun ta samun bullar cutar da suka hada da China da Vietnam da Philippines. An kashe aladu miliyan daya da dubu 200 a China kadai.

Labarai masu alaka