Shin Jonathan ya kulla yarjejeniya da APC ta Buhari?

Buhari
Bayanan hoto,

Zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon ya kai ziyarar ban girma a fadar shugaban kasa

Tun dai bayan da hukumar zaben jihar Bayelsa ta sanar da cewa dan takarar jam'iyyar APC, David Lyon ne ya lashe zaben gwamna da aka gudanar ranar Asabar a jihar, 'yan Najeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu kan yadda aka yi aka haihu a ragaya.

Kafin ranar Lahadi dai lokacin da hukumar zaben ta sanar da sakamakon zaben, jam'iyyar PDP mai mulki ta kwashe shekaru 20 tana jan ragamar jihar ta Bayelsa wato tun daga 1999.

Bugu da kari, kasancewar tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan wanda babban jigo ne a jam'iyyar PDP ya kara sa jama'ar kasar dasa ayar tambaya kan nasarar da jam'iyyar APC ta samu a jihar.

Hukumar zabe ta jihar Bayelsa dai ta bayyana Mista Lyon na APC a matsayin wanda ya samu nasarar bayan samun kuri'u 352,552, inda dan takarar jam'iyyar PDP, Mista Duoye Diri ke biye masa da kuri'u 143,172.

Sakamakon ya nuna girman tazarar da APC ta bai wa PDP, inda ta rubanya ta sau fiye da biyu.

Yanzu dai jihar Bayelsa ce ta farko a yankin Neja Delta da jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta karbe daga PDP.

Shin APC ta mamaye Bayelsa?

Tambayar da ke bakunan 'yan Najeriya kenan. To sai dai masu lura da al'amura irinsu Dokta el-Haroon Muhammad na kwalejin fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Kaduna na ganin ba haka al'amarin yake ba.

El-Haroon ya ce zai wuya a ce jam'iyyar APC duk kuwa da cewa ita ce ke da madafun iko a tarayya, ta iya yi wa jam'iyyar PDP irin hawan kawarar da ta yi mata a jihar, ba tare da wata makarkashiya daga cikin gida ba.

"Da ma ita siyasa kulle-kulle ce. Ita siyasa makirci ce."

Ruwa ba ya tsami banza

Sakamakon zaben Bayelsa ya nuna David Lyon na jam'iyyar APC ya ci kananan hukumomi shida daga cikin takwas, ciki har da karamar hukumar Ogbia ta tsohon shugaban Najeriya, Jonathan.

Ko da a Otouke garinsu tsohon Shugaba Jonathan jam'iyyar APC ce ta yi nasara kan PDP duk da kasancewar mahaifar tsohon shugaban ce.

Bisa la'akari da irin farin jini da karfin fada a ji da tsohon shugaban yake da shi a mahaifar tasa da ma sauran sassan jihar, wasu na ganin idan dai ba shugaban ne ya ba da kofa ba, to da wuya a yi wa jamiyyar irin wannan hawan kawara.

Rahotanni na alakanta rashin nasarar jam'iyyar PDP da rashin jituwa tsakanin gwamna mai barin gado, Seriake Henry Dickson da Goodluck Jonathan.

An dai ce rikici tsakanin mutum biyun ya samo asali ne tun daga fitar da mutumin da zai wakilci jam'iyyar PDP a zaben gwamnan.

El-Haroon Muhammad yana ganin "bakin jinin da Gwamna Seriaki Dikson yake da shi ka iya zama dalilin faduwar jam'iyyar ta PDP.

Ya kuma ce "akwai yiwuwar shi ma Jonathan ya bi sahun mai dakinsa, Dame Patience wadda ta fito kiri-kiri ta ce APC za ta zaba."

To sai dai wasu masu lura da al'amura na ganin Jonathan ya sakankance da harkar siyasa tun bayan da ya sha kayi a zaben shekarar 2015.

Me ya kai shugabannin APC wurin Jonathan?

Rahotanni sun nuna cewa a ranar Lahadi ne dai wata tawagar shugabannin jam'iyyar APC karkashin jagorancin gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru suka kai wata ziyara gidan Goodluck Jonathan a garin Otouke.

Wani dan jam'iyyar APC, Ileowo Kikiowo ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Gwamna Badaru wadda shi ne jagoran kamfe na jam'iyyar APC a zaben gwamnan na jihar Bayelsa, tare da Sanata Itang Enang sun ziyarci Goodluck Jonathan.

Wannan ziyara dai ta faru ne a daidai lokacin da jama'ar jihar ke cikin rudu kan mutumin da Jonathan zai mara wa baya kasancewar shi da Seriaki Dickson sun raba gari.

To sai dai Jonathan ya musanta rade-radin da ake yi cewa ya yaki jam'iyyarsa ta PDP a zaben gwamnan jihar.

Ziyarar Jonathan ga Buhari

Tun bayan amsar mulki daga hannun Goodluck Jonathan, ba a taba jin wata mummunar kalma ta fito daga bakin Shugaba Buhari kan Jonathan din ba duk da cewa gwamnatin Buhari ta sha nuna wa tsohuwar gwamnatin yatsa kan wasu tuhume-tuhume.

Sai dai a wasu lokutan baya, Shugaba Jonathan ya sha yin hannunka mai sanda ga gwamnatin Buhari duk da cewa shi ma bai taba kama suna ba.

To amma a baya-bayan ne Shugaba Buhari ya yi wata ganawa da magabacin nasa, Goodluck Jonathan a fadar gwamnati da ke Abuja.

Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya sanar da haka a shafinsa na Twitter cewa shugaban ya karbi bakuncin Jonathan a fadar gwamnati, sai dai bai fayyace dalilin ganawar ba.

Jonathan da Buhari dai sun kasance cikin sakin fuska da walwala yayin ziyarar.

El-Haroon ya ce "rade-radin da ake yi shi ne Jonathan zai koma jam'iyyar APC a jihar ta Bayelsa."

Ya kara da cewa bisa la'akari da yadda siyasar Najeriya ta bambanta da ta sauran kasashen duniya, babu mamaki idan wani tsohon shugaba ya koma jam'iyyar shugaban da ya kayar da shi.

"Idan ka lura da irin terere da ake yi wa Janar Sani Abacha cewa ya yi sata, ba laifi ba ne idan Jonathan ya rufa wa kansa asiri ya koma jam'iyya mai mulki."

Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda zababben gwamnan jihar ta Bayelsa zai tafiyar da mulki da kuma irin yadda alaka za ta kasance tsakaninsa da shugaba Jonathan.