Tottenham ta kori kocinta Mauricio Pochettino

A Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A bara ne kungiyar ta samu damar zuwa wasan karshe a gasar Zakarun Turai, inda ta sha kashi a hannun Liverpool

Tottenham ta sallami kocinta Mauricio Pochettino bayan fiye da shekara biyar yana jan ragamar kungiyar ta Premier.

Tsohon kocin Southampton, mai shekara 47, an nada shi a matsayin mai horas da 'yan wasan Tottenham a watan Mayun 2014.

A bara ne kungiyar ta samu damar zuwa wasan karshe a gasar Zakarun Turai, inda ta sha kashi a hannun Liverpool.

Sai dai a bana ta fara wasannin ta da kafar hagu, yayin da take mataki na 14 a teburin Premier.

Shugaban kungiyar Daniel Levy ya ce:

"Muna matukar bakin cikin yin wannan sauyin.Ba shawara ce da Tottenham ta yanke cikin sauki ko kuma hanzari ba. Sakamakon kakar bara da ta bana da aka samu abin takaici ne sosai."