Hotuna: Yadda sarkin Hausawan Turai ya nada hakimansa

Image caption Sarkin Hausawan Turai, Alh Sirajo Jan Kado ya nada hakimai takwas a masarautarsa da ke Paris
Image caption Sarkin Hausawan Turai tare da Marafan Hausawa kuma Hakimin London, Alhaji Muhammadu Sanusi da kuma Dan Isa, Dr Usman T Shehu
Image caption Hakimai takwas Sarki Jan Kado ya nada a ranar Asabar a fadarsa da ke Paris
Image caption Wadanda aka nada sun fito daga kasashe daban-daban na Turai
Image caption Sarki Jan Kado Na kokarin raya al'adun Hausawa a Turai
Image caption Akwai masu rike da sarautar Dan buran, da Sallama, Da Falaki da Shamaki da kuma Uban Doma
Image caption Masarautar na da Jakadiyar Sarki, da Giwar Sarki da kuma Gimbiyar Mawaka
Image caption An baiwa Fati Nijar sarautar Gimbiyar Mawakan Hausawan Turai
Image caption Baya ga wadanda aka nada sarautar, wasu sun halarci bikin nadin daga kasashe daban-daban na nahiyar Turai
Image caption An nada Jakadiya da kuma Giwar sarki
Image caption Masu rike da sarauta a masarautar kan sanya kaya irin na al'adar kowace masarauta da ke kasar Hausa
Image caption Wadanda aka nada wa sarauta sun hada da mata da maza daga yankuna daban-daban
Image caption Sarki Jan Kado Na kokarin raya al'adun Hausawa a Turai
Image caption A makonnin baya, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci masarautar a Paris inda ya jadadda sarautar Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Surajo Jan Kado
Image caption Daya daga cikin kofofin shiga fadar sarkin Hausawan Turai da ke Paris a kasar Faransa.

Labarai masu alaka