''Yata ke ceto na idan mijina yana duka na'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da matar da mijinta ke dukanta

Ku latsa lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar matar da Badriyya Tijjani Kalarawi ta BBC:

Hairiyya, wadda ba sunanta na gaskiya ba kenan, na daga cikin dubban matan da ke fuskantar cin zarafi daga wajen mazajensu.

Matar wadda 'yar wani gari ce a arewacin Najeriya, ta shaida wa BBC cewa tun tana amarya a farkon aurenta, mijinta ke yi mata duka da wulakanci salo-salo ba tare da ta san ainihin laifin da ta yi masa ba.

Ta ce har yanzu da auren ke neman cika shekara goma tare da samun albarkar 'ya'ya, babu wani sauyi da ta samu ta fuskar daina duka ko zagin ta da mijin ke yi.

"A wasu lokutan idan yana dukana, 'yata mai shekara takwas ce ke zuwa tana cetona tana kuka tana Abba ka daina dukan Umma," cikin kuka Hairiyya ta gaya wa BBC.

An yi wannan hira ne da ita albarkacin ranar yaki da cin zarafin mata a sassa daban-daban na duniya.

Ranar yaki da cin zarain mata a duniya

Majalisar Dinkin Duniya ce ta kebe duk ranar 25 ga watan Nuwamba don yaki da duk nau'o'in cin zarafin mata.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa mace daya cikin mata uku ta taba fuskantar wani nau'i na cin zarafi walau fyade ko duka ko musgunawa ko auren wuri ko kuma kaciya.

An fitar da wadannan alkaluman ne, don bankado dukkan nau'ukan cin zarafi da duniya ba ta farga da su ba.

A yunkurin su na bayyana wa duniya hali da suke ciki, mata a sassa daban-daban kan kafa kungiyoyi da kuma yin gangami don magana da murya daya.

Sai dai kuma duk da hakan, da yawansu musamman a nahiyar Afrika kan zabi yin shiru, kan batutuwan da suka shafi cin zarafi maimakon sanar da hukumomin da suka dace domin daukar mataki.

Dalili kuwa shi ne gudun jin kunya da kyama da kuma rashin tabbas wajen samun adalci daga hukumomi.

'Mahaifina ya min duka kawo wuka'

Wannan dalili na daya daga cikin abin da ya sa ita ma Hairiyya ta gwammaci ci gaba da zama cikin wannan hali, ba don tana son auren ba.

"A duk lokacin da na tambaye shi ko ina masa wani laifi ne da ban sani ba, to a ranar sai na gamu da wani sabon bacin ran.

"Wallahi yanzu idan ya fita daga gida kamar an sani a aljanna, amma da ya dawo zan shiga cikin bacin rai. Ina kuka ina rokon Allah ya fitar da ni daga wannan ukuba," in ji ta.

Hairiyya ta ce babban abin takaicin shi ne yadda iyayenta ba sa tsayawa ma sam su ji matsalarta balle su taimaka mata.

"Akwai ranar da na kai wa mahaifina korafi shi da waliyyina, Wallahi a gaban mijin nawa baban ya min dan banzan duka ko nasiha ba a yi masa ba haka na ci dan banzan bugu.

"To iyayena ma ba su taimake ni ba waye zai taimake ni?" Ta karasa cikin kuka.

Kawo karshen matsalar

Majalisar Dinkin Duniyar dai na fatan ganin an kawo karshen dukkan nau'uka na cin zarafin mata nan da shekara ta 2030.

Shin ko za ta iya cika wannan buri nata, idan aka yi la'akari da yawan rahotannin musguna wa matan da ake samu a ko wace rana?

Lokaci ne kadai zai nuna.