An kama shugaban Gidan Yarin Kiri-Kirin Legas kan 'damfarar' N360m

Hope Olusegun Aroke is pictured in a handout image provided by the Economic and Financial Crimes Commission Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Hope Olusegun Aroke yana zaman shekara 24 a gidan yarin

An kama shugaban Gidan Yarin Kiri-Kiri da kuma wani likita da ke aiki a wajen a Legas da ke kudancin Najeriya, sakamakon zarginsu da ake yi da barin wani mutum da ke tsare ya dinga damfara ta intanet.

Hope Olusegun Aroke ya yi damfarar dala miliyan daya, kwatankwacin naira miliyan 360, a yayin da yake tsare a gidan yarin - kan hukuncin damfara.

Ya samu damar amfani da wayarsa da kuma intanet.

Tun farko an kama shi ne a shekarar 2012 aka kuma yanke masa hukunci kan amfani da kudin bogi.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC, ta ce an kam mutanen biyu ne saboda bayar da rahoton lafiya na karya da ya bai wa Aroke damar fita daga gidan yarin don zuwa wani asibitin 'yan sanda a duba shi.

A wata sanarwa da EFCC ta fitar ta ce, "A ranar Litinin 25 ga watan Nuwambar 2019 ne jami'an hukumar suka kama wadanda ake zargin da Emmanuel] Oluwaniyi, shugaban Gidan Yari mai cike da tsaro na Kirikiri da kuma Hemeson Edson] Edwin, wanda ke kula da asibitin gidan yarin.

Hukumar ta kara da cewa Aroke na daya daga cikin daliban Najeriya a Malaysia da ba su kammala karatu ba wadanda suka kware a damfara, kuma EFCC ta kamashi a karshen shekarar 2012 sakamakon binciken sirri da aka gudanar.

Ya yi ikirarin cewa shi dalibin kimiyyar kwamfuta ne a Jami'ar Kuala Lumpur Metropolitan, amma ya zamo "gagarumin dan damfara a kasashen biyu."

Bayan da aka kwantar da shi a wani asibitin 'yan sanda, hukumomi sun ce Aroke ya koma wani otal inda ya dinga ganawa da mutane.

Ya yi amfani da wani sunan karya Akinwunmi Sorinmade, ya bude asusun ajiya a banki har biyu, ya kuma sayo motar alfarma da gida a lokacin da yake tsare a gidan yari, a cewar EFCC.

Labarai masu alaka