Dokar kalaman kiyayya a Najeriya da martanin 'yan kasa

Sanata Ahmed Lawan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dokar ta tsallake karatu na farko a Majalisar Dattawa

Sanata Sabi Abdullahi na majalisar dattijan Najeruya ya fara kaddamar da kudirin dokar kalaman kiyayya ne (Hate Speech Bill) tun a watan Maris na 2018, kuma tun daga wannan lokaci ne mutane suka nuna damuwa game da abin da dokar ta kunsa.

"Kudirin ya mutu ne lokacin da wa'adin majalisa ta takwas ya kare. Da Allah ya yi mani dawowa majalisa ta tara sai na ga cewa maganar kalaman kiyayya abu ne da ya zama wajibi Najeriya ta kawo karshensa," Sabi Abdullahi ya fada a wata hira da Channels TV.

Sanata Sabi Abdullahi wanda shi ne mataimakin mai tsawatarwa na Majalisar Dattawan Najeriya, ya sake bijiro da kudirin gaban majalisar da sunan 'National Commission for the Prohibition of Hate Speeches Bill, 2019 (SB. 154)'.

A ranar 12 ga watan Nuwamban 2019 ne kuma ta tsallake karatu na farko. Yanzu tana jiran karatu na biyu - duk da cewa ba a saka ranar yin hakan ba.

Wannan dokar 'yar uwa ce ga wata dokar ta "Protection from Internet Falsehood and Manipulation Bill, 2019 (SB 132)", wadda 'yan Najeriya suke yi wa lakabi da 'Social Media Bill'.

Ita kuma tana yunkurin tantancewa tare da yin hukunci ga abin da mutane suke wallafawa a shafukan sada zumunta, wadda Sanata Muhammad Sani Musa daga jihar Neja ya gabatar.

Tuni ta tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawan.


Tanadin dokar

Idan aka kaddamar da ita a matsayin doka, duk wanda aka samu da aikata laifin kalaman kiyayya zai fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Tanadin dokar ya hada da kirkirar wata hukuma ta musamman mai zaman kanta domin kula da laifukan kiyayya mai suna 'National Commission for the Prohibition of Hate Speeches'.

Amma a wani bayani da ya fitar ga manema lanbarai ranar Lahadi, Sabi Abdullahi ya ce za su yi wa wasu sassan dokar kwaskawarima "musamman ayar da ta tanadi hukuncin kisa wanda shi ne abin da 'yan Najeriya suka fi damuwa a kai".


Me yasa ake son yin dokar?

"Tashe-tashen hankulan da kalaman kiyayya suka haifar sun haddasa rasa rayukan mutane da dama, idan dai mutuwa ba ta da dadi to ya kamata mu hana kalaman kiyayya," Sanata Sabi Abdullahi ya fada.

Ya ci gaba da cewa: "Mutane da dama sun fada cikin kalaman kiyayya ba tare da sun sani ba. Hikimar kafa wannan hukuma ita ce, a tattaro mutanen da suke da kwarewa domin tattaunawa da yin sulhu.

"Akasarin wadanda suke aikata wannan laifi fa manya ne, wadanda jama'a ke sauraronsu, suke da fada-a-ji.

"Ya sha faruwa da yawa, inda za ka ga wani mutum ya yi wata maganar kiyayya kan wani addini ko kabila nan take ka ga an kashe wani.

"An saba a kasar nan duk sanda aka samu rikicin bayan zabe sai dai a kafa wani kwamiti na bincike, me ya sa ba za mu kafa hukuma ta musamman ba domin yin wannan aikin?"


Manyan kasa na neman mafita game da kalaman kiyayya

Hakkin mallakar hoto @ProfOsinbajo
Image caption "Muna kallon ta (dokar) a matsayin tamkar dokar yaki da ta'addanci," in ji Farfesa Osinbajo Mataimakin Shugaban Najeriya

A shekarar da ta gabata, mataimakain shugbaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kamanta dokar kalaman kiyayya da dokar yaki da ta'addanci.

"[Gwamnati] ta ja layi kan kalaman kiyayya, in ji shi. "Ba za a lamunta ba, muna kallon ta (dokar) a matsayin tamkar dokar yaki da ta'addanci kuma hukunci zai biyo baya."

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi kira da "a fuskanci matsalar gaba-gadi" yayin da yake magana a wurin wani taro da aka yi wa lakabi da 'Kalaman Kiyayya: Kamo Bakin Zaren Kafin Abubuwa Su Rincabe' (Hate Speech: Halting the Tide Before it is Too Late).

Yayin da yake alakanta kalaman kiyayya da irin abin da ya faru a kasar Rwanda, ministan yada labarai Lai Mohammed ya ce: "A Najeriya, irin kiyayyar da ake yadawa a rediyo abin firgici ne.

"Idan ka kama gidajen rediyo da dama sai ka firgita da irin abin da ake yadawa na rashin kulawa wanda ke haddasa fitina a kasarmu mai cike mabambantan al'adu da addinai."


Me 'yan Najeriya ke yi?

Image caption Masu zanga-zangar a Abuja sun yi kira ga shugabannin majalisar tarayya da kada su yi dokar

'Yan Najeriya ba su bar wannan yunkurin doka ya tafi haka ba tare da abin da aka saba ba: ko dai zanga-zanga a fili ko kuma a shafukan sada zumunta, wanda dukkansu sun faru.

A ranar Laraba 28 ga watan Nuwamba ne daruruwan 'yan Najeriya suka yi wa ginin Majalisar Dattawa tsinke domin yin zanga-zangar kin jinin daftarin dokar a Abuja.

Image caption A jihar Legas kuwa dan majalisa Honorabul Yusuf ne ya tarbi masu zanga-zangar a madadin kakakin majalisar
Image caption Wadanda suka fito a jihar Legas ba su kai yawan na Abuja ba

A jihar Legas kuwa dan majalisa Honorabul Yusuf ne ya tarbi masu zanga-zangar a madadin kakakin majalisar dokokin jihar, sai dai ba su da yawa kamar na Abuja - Wakilin BBC ya ce ba su wuce mutum 50 ba.

Wata kungiyar matasa mai rajin kafa dimukradiyya da mulki na adalci mai suna EIE ta kaddamar da wani kamfe a Twitter, inda take amfani da maudu'in #SayNoToSocialMediaBill tana kiran sunayen sanatoci tare da jan hanakalinsiu game da dokar.

Revolutionary Effa (@DrEffaB) cewa ya yi ga sanatan da ya dauki gabarar dokar kalaman kiyayya, ku yada shi har mahukuntan ksar Amurka su gani domin hana shi biza da shi da iyalinsa.