Dabbobin da ba za mu kara gani ba... da kuma wadanda suka sake dawowa duniya

Kasusuwan dinosaur a cikin rairayi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dabbar dinosaurs ta shude a doron kasa sama da shekara miliyan 66

Wasu lokutan mu kan yi tunanin da wuya abin da ya shude ya dawo, musamman dabbatar dinosaurs, amma hakan ka iya faruwa.

Kamar yadda gidauniyar kare hakkin dabbobi ta tabbatar, a kowacce shekara sama da tsirrai da tsuntsaye 10,000 ne ke bacewa a doron kasa.

Hukumar ta ce zai yi wuya a tabbatar da ainahin adadi sai dai hasashe, saboda rashin sanin adadin tsirrai da tsuntsayen da ke wurin da ake bincike akai ba.

Ya yin da ake gab da fara bikin tunawa da abubuwan da suka bace a ban kasa a ranar 30 ga watan nan, za mu yi waiwaye da duba kan rayuwar wasu daga cikin dabbobi da suka yi rayuwa a baya, amma a yanzu babu su.

Nau'in birin Waldron Red Colobus (Ghana da Ivory Coast)

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan nau'in birin da aka fi samu a kasar Zanzibar mai suna Red Colobus, na daya daga cikin dangin birrai da suka bace a ban kasa, lokaci na karshe da aka ga irinsu shi ne shekarar 1978

An yi amanna da cewa wannan nau'in birin ya rayu a duniya tun shekaru 2000 da suka wuce.

Ana wa birin lakabi da Mis Waldron Red Colobus, da ke rayuwa tsakanin iyakokin Ghana da Ivory Coast, sai dai ana ganin cewa birin ya bace tun a farkon shekarun 2000.

Birin wanda aka fi samun sa a kan iyakar Ghana da Ivory Coast, na da banbanci da birrai ta hanyar rashin babban dan yatsan hannu.

Dabbace mai nutsuwa da ke rayuwa cikin kungiya tare da darewa saman bishiya, an tirsasa wa birrai zama a ban kasa a lokacin da bil'adam suka fara sare bishiyoyi.

Yayin da dazukanmu ke kara tsukewa, su ma nau'in birin suka fara raguwa, rashin haifarsu da yawa ta hanyar hada aure ya taimaka wajen bacewarsu.

Nau'in kifin Dolphin da ake samu a kogin Yangtze na China

Image caption Nau'in kifin dolphin na kasar China da ake kira baiji, an yi amanna shi ne kifi mafi dadewa a ruwa ana samunsa kogin Yangtz na kasar

A shekarar 2006 ne China ta nuna nau'in kifin dolphin da take da shi a Kogin Yangtze, ya banbanta da sauran 'yan uwansa da muka saba gani wanda jikinsu baki ne sidik mai kyalli da santsi musamman idan suna ninkaya a kwami.

Shi wannan nau'in jikin shi ruwan toka ne, ba ya kyalli amma kuma akwai santsi a jikinsa.

Yana da tsawo sosai, an fi ajiye shi a wuri mai amsa kuwwa. Babban abin da ya kara banbanta su da sauran shi ne yana iya gano kifi komai nisan inda yake idan dai cikin ruwa guda suke.

Sai dai kash, yana fuskantar barazanar karewa, saboda kwale-kwale da manyan jiragen ruwa da ke kara-kaina a Kogin Yangtze, da tarkacen abubuwan da ke gurbata muhalla da ake jibgawa cikin kogin.

Yana cikin hadari saboda rashin sabo da sauyin da ya kawo masa ziyara lokaci guda.

Dabbar monk seal (da ake samu tsakanin kasashen Jamaica da Nicaragua)

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dabbar Seals pup mai rayuwa a yankin Caribbean

An fi samun wannan nau'in dabba ta ta Seals Pup a Kogin Mexico, da gabar tekunan gabashin tsakiyar Amurka, da tekun arewacin kudancin Amurka.

Sai dai suna fuskantar barazanar karewa, saboda yadda ake farautarsu don jikinsu makare yake da mai, sannan suna mutuwa sakamakon kame abincinsu wato kifaye da ake yi.

Tun daga shekarar 1952 suke ja da baya, kuma an fi samunsu a yammacin Serranilla tsakanin kasashen Jamaica da Nicaragua.

Dabbar ruwa Alabama Pigtoe (da ake samu a Amurka)

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption River mussels da aka fi samu a jamhuriyar Czech, suna kamanceceniya da giant clams

Wannan nau'in dabbar ruwan ta mussel na rayuwa a Tekun Alabama, a Amurka har zuwa shekarar 2006.

An sanya masa sunan ne sakamakon kamanni da kafar alade, abubuwan da ake sanyawa cikin tekunan mu da ke gurbata muhalli na kashe su, don haka ake ganin kamar ba za su yi tsawon rai a duniya ba.

Shafewarsu a ban kasa na nufin hadarin da tekunanmu ke ciki sakamakon gurbacewarsa, sakamakon sinadarai masu hadari da masana'antu ke zubawa yana kara ta'azzara rashin lafiya ga mazauna kusa da irin tekunan.

Dodo (da ake samu a kasar Mauritius)

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dodo na daga cikin alamun da suka tabbatar dan adam ya taimaka wajen bacewarta

Abu ne banbarakwai a ce an girmama tsuntsu, amma saboda wasu dalilai tsuntsun dodo na daga cikin wadanda suka dade da shudewa a ban kasa ba ya ga dabbar dinosaurs wadda kusan kowa ya san da ita.

Shekaru aru-aru doguwar tsuntsuwar mai kama da agwagwa ta taba rayuwa a tsuburin kasar Mauritius, ba tare da doggaro wata nau'in dabba ko tsuntsu ba a matsayin abinci.

Bayan bil'adama sun fara zama Mauritius, sun taho da dabbobi daban-daban da sauran nau'in abinci dan haka dodo ba ta dade a kasar ba.

Tsuntsun dodo na karshe da aka gani shi ne a shekarar 1700.

Dabbar ruwa mai Steller's Sea Cow (An fi ganinta a Alaska da Russia)

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jirgin ruwa da masanin tsirrai George Steller, shi ya gano wannan dabbar a shekarar 1741 a tekun Bering tun kafin a fara farautarta

Da kun taba cin karo da dabbar ruwa mai suna Steller's Sea Cow da kuwa kun san abubuwa da dama akanta.

Jikinta na yanayi da kifi tarwada, kuma tana da nutsuwa idan tana tafiya cikin ruwa, amma fa katuwar gaske ce. Bincike da bayanan da aka tattara sun nuna tana da girma da tsawon mita tara.

Ita ma jikinta makare yake da maiko da lallausan nama, watakila shi ne dalilin da rayuwarta ta zama cikin hadari saboda farautarta da ake yi.

Namanta yana da dandanon jan nama da ka jika shi cikin kayan hadi da man almond.

Yawan sauyin abinci, da farauta hadi da gurbacewar muhalli na daga cikin abin da ya janyo bacewar Teller Sea Cow kamar yadda ya faru da tsuntsun dodo.

Dabbar Quagga (da ake samu a Afirka Ta Kudu)

Image caption A shekarar 1882 ne dabbar Quagga ta mutu a gidan ajiye namun daji na Artis Zoo da ke Amsterdam

Kyawun da tsohuwar dabbar Quagga ke da shi abin kallo ne.

Wannan dabbar da aka fi samunta a nahiyar Afirka, tana da wasu zane-zane kwatankwacin irin zanen jikin jakin dawa mai launin fari da ruwan kasa.

Masu farautar namun daji da kwarjinin dabbar ke daukar hankali ne suka taimaka wajen bacewarta a ban kasa a shekarar 1880 da aka yi mata ganin karshe.

Gwanki (Ireland)

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamar yadda gwanki yake, amma wannan babba ne

Yawancin dabbobi ko tsirrai ko tsuntsaye suna kama ko yanayi da juna, amma wasu lokutan ba sosai ba. Wannan nau'in gwankin ana samunsa ne a kasashen Turai.

Kamar dabbar Mammoth mai yanayi da giwa, kama daga haure har girma da zungureren hancin, abin da ya banbanta su shi ne jikinta cike yake da gashi mai tsawon gaske.

Ta shafe a ban kasa shekararu 7,700 da suka wuce, watakil saboda sauyin yanayi da farauta.

Farar mikiya mai doguwar jela 'yar Birtaniya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Farar mikiyar mai doguwar jela ana samunta a kasar Norway

A farkon karni na 20 ne farar mikiyar ta bace a Birtaniya, amma ba ta dade ba ta sake dawowa.

Wannan mashahuriyar tsuntsuwar, tana da manyan fuka-fukai masu tsawon sama da mita biyu. Shekaru da dama akai ta farautarta a Birtaniya, kai ba farauta kadai ba har da kisan gilla kuma hakan haramun ne.

A lokacin da aka auna haramcin farautar farar mikiyar, lokaci ya kure don kuwa ta ma kusan karewa.

Amma tana rayuwa a wasu kasashen Turai, kuma watakil ta sake komawa Birtaniya.

Sai dai ba kowacce dabba ce ke samun dama irin ta farar mikiya mai doguwar jela ba.

Labarai masu alaka