Me doka ta ce kan fanshon tsoffin gwamnoni a Najeriya?

Matawalle

Tun dai bayan da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari ya nemi gwamnan jihar mai ci, Bello Matawalle da ya biya shi dukkan hakkokinsa da doka ta tanada da suka hada da fanshon naira milyan 10, 'yan Najeriya ke ta ce-ce-ku-ce kan halasci ko akasin fanshon ga tsoffin shugabanni.

Masana irin su Malam Kabir Dakata na kungiyar CITAD ya ce kididdigar da suka yi ta nuna "za a iya amfani da naira milyan 10 wajen biyan ma'aikata 333 albashi mafi kankanta na wata daya a jihar."

Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewa fiye da jihohin Najeriya 20 ne suke da dokar fansho ga tsoffin gwamnoni da mataimakansu da shugabannin majalisun jihohin.

To sai dai kudaden fanshon jihohin Zamfara da Kaduna ne suka fito fili a baya-bayan nan, inda a jihar Zamfara ake bai wa tsoffin shugabannin jihar naira milyan 10 a duk wata guda.

Ita kuwa jihar Kaduna, kamar yadda tsohon gwamnan jihar, Malam Balarabe Musa ya shaida wa BBC, yana karbar naira 741,000 a duk wata, a matsayin fansho.

Har wa yau, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido yabayyana cewa naira 667,000 ya ke karba.

Sule Lamido ya fadi hakan ne yayin wani martani da ya mayar ga labarin fanshon Balarabe Musa, da BBC ta wallafa a shafinta na Twitter.

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Alhaji SUle Lamido ya mayar da martani a shafin BBC na Twitter

Wani bincike da BBC ta yi bai gano hakikanin yawan kudin da tsoffin shugabanni ke karba ba a jihar Kano kasancewar abubuwa ne da dama a cikin kunshin fanshon nasu kamar haka:

 • Gida mai daki shida ga gwamna, inda mataimakinsa kuma zai samu gida mai daki hudu
 • Ofis mai dauke da kayan aiki
 • Albashi kamar na gwamna mai ci
 • Samun kulawar lafiya
 • Hutun kwana 30 a duk kasar da yake so
 • Direbobi guda biyu ga gwamna

Mene ne fansho?

Dokar fansho ta Najeriya ta 2004 wadda aka yi wa gyaran fuska a 2014 ta tanadi:

 • Ma'aikaci zai bayar da akalla kaso 10 na albashinsa
 • Gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu za su bayar da akalla kaso takwas kan abin da ma'aikacinsu ya biya.

Sai dai dokar ta kara da cewa akwai damar sake yin waiwaye ga yawan kudin ma'aikatan lokaci zuwa lokaci.

Image caption Shugaba Buhari ya sha fadin cewa zai rage yawan kashe kudaden gwamnati

Tsoffin shugabanni da dokar fanshon Najeriya

Dokar fanshon Najeriya dai ba ta yi wani tanadi na musamman ba ga wani mai rike da mukami lokacin da zai bar kujera.

Sai dai hukumar tattara kudaden shiga da raba su ta Najeriya wato Revenue Mobilisation Allocation and Fiscal Commission (RMAFC) ta yi tanadi ga masu rike da kujerun siyasa a lokacin barin ofis.

Hukumar ta tanadi cewa za a ba su kaso 300 na gwargwadon albashinsu na shekara guda a matsayin sallama.

Tanade-tanaden na RMAFC sun kuma ce tsoffin gwamnoni na da abubuwa kamar haka:

 • Sabbin motoci da za a rinka sauyawa a duk tsawon shekaru uku ko hudu.
 • Gina musu gida a babban birnin jiha ko kuma birnin Abuja.
 • Biya musu yin hutu na kwanaki 30 a kasar waje da kuma kula da lafiyarsu da iyalansu.

Wannan na nufin kenan dokar fanshon tsoffin shugabanni a jihohi ta yi karo da dokar fansho ta Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a 2014 da kuma tanade-tanaden hukumar RMAFC.

Masana sun yi ca kan dokar fansho a jihohi

Malam Kabir Dakata na CITAD ya ce lokacin da jihohi suka fara aiwatar da dokar fansho sun fara a kan gwamnoni kawai, kafin daga bisani su shigar da mataimakansu da ma shugabannin majalisa.

Kabir Dakata ya ce "idan aka yi wasa to za a kai lokacin da za a yanka wa kwamishinoni da sauran 'yan majalisu fansho.

"Al'amarin da zai janyo kashe kudade makudai ga tsirarun 'yan kasa."

Shi ma shugaban kungiyar CISLAC mai fafutaka kan rashawa da cin hanci a Najeriya, Awwal Rafsanjani ya yaba wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle kan soke dokar bai wa tsoffin shugabannin fansho.

Rafsanjani ya kuma bukaci gwamnatin Shugaba Buhari da sauran jihohin Najeriya da su yi koyi da gwamnan na jihar Zamfara.

Masu rajin ganin an kawar da rashawa da cin hanci a Najeriya na ganin idan ba a yi wa tufkar hanci ba a yanzu to za a kai ga lokacin da wani kaso mai tsoka na kasafin manyan ayyuka.

Kbairu Dakata na CITAD na ganin lokaci ya yi da ya kamata a yi koyi da gwamnatin jihar Zamfara wajen soke fansho ga tsoffin gwamnoni.

"Idan a ka yi duba ga irin makudan kudaden da suke karba ta hanyoyi da dama da suka hada da kudaden tsaro, za mu fahimci ba su makudan kudi a fansho bai kamata ba."

An dai samu irin wannan ce-ce-ku-ce a 2017 lokacin da Najeriya ta fada yanayin karyewar tattalin arziki, a wasu watanni biyu kasar ta kashe wa tsoffin gwamnonin jihohi 21 kudi fiye da naira bilyan 40 da sunan fansho.

A baya-bayan nan ne dai shugaba Buhari ya sanar da tsuke bakin aljihun gwamnati, al'amarin da ya sa shugaban ya rage yawan ma'aikata masu taimaka wa mataimakinsa, farfesa Yemi Osinbajo.

Abin jira a gani dai shi ne ko gwamnatin Najeriya za ta amsa kiraye-kirayen 'yan Najeriya wajen daukar matakin kan fanshon tsoffin gwamnoni da mataimakansu.

Labarai masu alaka