Ba mu hana amfani da waya ba - FRSC
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ba mu hana amfani da Google Map ba - FRSC

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Hukumar kare hadurra ta kasa ta musanta cewa ta hana amfani da manhajar Google Maps ko kuma manhaja mai nuna taswirar wurin da mutum yake, wato GPS.

Jami'in na hukumar ya shaida wa BBC cewa ba a fahimci maganar da kwamandansu na Abuja ya yi ba.

Ya ce za a iya amfani da GPS ko wasu manhajoji masu kwatance ta hanyar amfani da murya.

Labarai masu alaka